An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo
Published: 13th, April 2025 GMT
Jami’an tsaron Jihar Edo sun sake kama wasu mafarauta hudu daga Kano, makonni kadan bayan kisan gilla da ’yan bangar Jihar Edo suka yi wa ayarin wasu mafarauta 16 daga jihar Kano a jihar.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, ta ce mafarautan da aka kama sun fito ne daga Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano, kuma suna dauke da bindigogin toka guda uku, da adduna da wukake a lokacin da aka kama su.
Kakakin ’yan sanda an jihar, CSP Moses Yamu, ya ce kanawan da aka kama mafarauta ne ba kamar yadda ake yadawa a kafofin sada zumunta cewa makiyaya ba ne.
Ya bayyana cewa jami’an kungiyar tsaro ta Jhar Edo ne suka kama mafarautan sannan suka damka su ga ’yan sanda inda ake yi musu tambayoyi a ofishin ’yan sanda da ke yankin Ikpoba Hill.
’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje da Zamfara A daina cutar ’yan Najeriya ta hanyar rabon kayan tallafi Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken TinubuYa ce an, “An kama mafarautan da suka fito daga Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa yankin Uvbe da ke Karamar Hukumar Orhionwon a Jihar Edo. A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike.”
Da haka Kwamishinan ’yan sandan jihar, Monday Agbonika, ya gargadi jama’ar jihar da su guji yada abin da ba gaskiya ba ne game da lamarin, domin yana iya tayar da zaune tsaye.
Idan ba a manta ba, a cikin watan Ramadan, gab Sallah Karama ne ’yan banga suka yi wa wasu mafarauta 16 daga Jihar Kano da ke hanyarsu ta komawa gida hutun sallah kisan gilla a yankin Uromi da ke jihar, lamarin da ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya, inda har yanzu ake kokarin shawo kansa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda mafarauta Tsaro wasu mafarauta
এছাড়াও পড়ুন:
An gano motar da aka sace a Gidan Gwamnatin Kano
’Yan sanda a Jihar Kano sun gano wata mota ƙirar Toyota Hilux mallakar ofishin mataimakin gwamnan jihar, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, wadda aka sace kwanan nan a harabar gidan gwamnati.
Majiyoyi daga fadar Gwamnatin Kano sun ce an sace motar ce cikin dare, lamarin da ya kai ga tsare direban da motar ke hannunsa, Shafiu Sharp-Sharp a matsayin ɗaya daga cikin ababen zargi.
Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga — Ronaldo Troost-Ekong ya gargaɗi Super Eagles kan wasan da za ta fafata da GabonSai dai wata sanarwa da ofishin mataimakin gwamnan ya fitar, ta ce jami’an tsaro sun gano motar da safiyar wannan Larabar bayan wani aikin haɗin gwiwa na gaggawa da aka gudanar.
Sanarwar ta ce an kama wanda ake zargi da satar motar, Ya’u Gezawa, wanda yanzu haka yana taimaka wa jami’an tsaro wajen bincike.
Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu, ya bayyana lamarin a matsayin cin amanar aiki, tare da jinjinawa ’yan sanda bisa gaggawar da suka yi wajen gano motar da kama wanda ake zargi.