Aminiya:
2025-07-07@18:11:20 GMT

Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka

Published: 18th, March 2025 GMT

Ƙungiyar Hamas ta ɗora alhakin hare-haren da Isra’ila ta ƙaddamar yau Talata a Zirin Gaza kan Amurka.

A wata sabuwar sanarwa da Hamas ta fitar, ta ce Amurka ce ke da “alhakin kisan gillar” da aka yi a Gaza bayan da ta bayyana cewa Isra’ila ta shaida wa Amurka shirinta na kai hare-haren gabanin kai harin.

Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza

Sanarwar ta ce hakan ya “tona asirin ƙaryar da suke yi na iƙirarinsu kan damuwa da kawo ƙarshen yaƙin.

“Muna buƙatar ƙasashen duniya su ɗauki matakin gaggawa na kama masu aikata laifukan yaƙi da masu goya musu baya,” in ji Hamas.

A gefe guda kuma kafar yaɗa labarai da ke da alaƙa da Hamas, mai suna Filastin, ta ce an kashe jami’an gwamnatin Hamas huɗu a hare-haren Isra’ila.

Hazalika, shugaban hukumar lafiya da Hamas ke jagoranta, Munir al-Barsh ya ce mutane fiye da 660 aka jikkata a hare-haren, kuma wasu da dama na ƙarƙashin ɓaraguzai.

Majiyoyin kiwon lafiyar Gaza sun shaida wa gidan Talabijin na Al Jazeera cewa fiye da mutane 400 ne aka kashe, kuma mafi yawancinsu mata da ƙananan yara da kuma dattawa.

Harin wanda ke nuna kawo ƙarshen yarjejeniyar zaman lafiyar da aka ƙulla tsakanin Isra’ila da Hamas a watan Janairu, Isra’ila ta ce ta ƙaddamar da shi ne bayan da Hamas ta ƙi sako ragowar mutanen da ta yi garkuwa da su.

Wani jami’in Isra’ila ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, za su ci gaba ta kai hare-hare har sai sun kawar da shugabannin Hamas da gine-ginensu da kuma kayan aikinsu.

Fadar White House ta bakin sakatariyar yaɗa labaranta Karoline Leavitt, ta ce sai da Isra’ila ta sanar da ita, kafin ɗaukar matakin kai harin.

“Isra’ila ta sanar da gwamnatin Trump da fadar White House kan harin da suka kai Gaza a daren yau, kamar yadda shugaba Trump ya bayyana Hamas da Houthis da kuma Iran, da ke neman addabar Isra’ila har ma da Amurka, za su ɗanɗana kuɗarsu.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Falasɗinawa Isra ila Isra ila ta

এছাড়াও পড়ুন:

Jaridar Telegraph: Makaman Iran Masu Linzami Sun Sauka Kai Tsaye Akan  Cibiyoyin Sojan Isra’ila Guda 5  

A wani rahoton musamman da jaridar ” Telegraph” ta Birtaniya ta buga,  ta amabci cewa; makamai masu linzami da Iran ta harba wa Isra’ila sun sauka kai tsaye akan wasu muhimman cibiyoyin soja.

Jaridar ta kara da cewa; Mahukuntan Isra’ila ba su bayyana wa duniya wadannan wuraren da makamai masu linzamin su ka fadawa ba, saboda aiki da dokar soja ta Sakaye labaran wuraren da aka kai wa hare-hare.

Rahoton jaridar ya ce, ya sami bayanai ne daga hotunan tauraron dan’adam na jamiar Jahar Oregon da suka saba yin aiki da irin wadannan bayana da suke tarawa domin gano barnar da aka yi a wuraren yaki.

Rahoton ya ci gaba da cewa cibiyoyin sojan da Iran ta kai wa harin, a baya ba a yi Magana akansu ba, sai yanzu kuma suna a cikin yankunan arewa, kudanci da tsakiyar ne. Daga cikin  wuraren da akwai sansanin sojan sama mafi girma, cibiyar tattara bayanai na sirri, da kuma wata cibiya ta ajiyar kayan yaki.

A jiya juma’a sojojin HKI sun ki amsa tambayar jaridar ta Telegraph akan zurfin asarar da hare-haren na Iran su ka yi wa cibiyoyin nasu.

Sai dai kuma jaridar ta ce, wadannan sabbin cibiyoyin sojan da ake Magana makamai masu linzami na  Iran sun suka a cikinsu,kari ne akan wasu 36 da Iran din kai wa farmaki, wadanda na’urorin da HKI take takama da su na kakkabo makamai, su ka kasa tare su, kuma sun yi barna mai girman gaske.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Reuters: Amurka Tana Da Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza
  • Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Lardin Hodeidah Na Kasar Yemen
  • Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Mamayar Isra’ila Kan Kasar Yemen
  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce Kungiyar ECO Ta Yi Tir Da Hare-Haren HKI Kan Kasarsa
  • Jaridar Telegraph: Makaman Iran Masu Linzami Sun Sauka Kai Tsaye Akan  Cibiyoyin Sojan Isra’ila Guda 5  
  • Kungiyar Hamas Ta Sanar Da Matsayinta Kan Shirin Dakatar Da Bude Tsakaninta Da Gwamnatin Mamayar Isra’ila
  • Kungiyar Hamas Ta Ce Ta Amince Da Tattaunawa Don Kawo Karshen Yaki A Gaza
  • Shugaban Amurka Yace Yana Jiran Amsar Hamas Cikin Sa’o’i 24 Masu Zuwa Don Tsagaita Wuta Na Kwanaki 60
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kashe Masu Neman Karbar Kayan Agaji A Gaza