Aminiya:
2025-11-02@19:57:08 GMT

Turji: Sai ka sako mutanen da ka sace za a yi sulhu — Gwamnatin Sakkwato

Published: 7th, July 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ƙalubalanci jagoran ’yan bindiga Bello Turji, wanda ke neman sulhu, da cewa idan da gaske yake yi, to ya sako duk mutanen da ya yi garkuwa da su, ya daina kai hare-hare, kafin ta zauna da shi.

Mashawarci na musamman ga gwamnan Sakkwato a kan sha’anin tsaro, Kanar Ahmed Usman ne ya bayyana hakan baya yaɗuwar wani bidiyo da Turji ya saki, wanda a ciki yake neman a yi tsakaninsa da gwamnati.

Ɗan ta’addan wanda ya addabi yankunan jihar da makwabta ya saki bidiyon ne kwanaki kaɗan bayan jami’an tsaro sun kashe wasu gaggan kwamandojinsa da Faransa sama da 100.

Kamar Ahmed, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa babu yadda za a tabbatar cewa neman sulhun Turji ba ta fatar baki ba ne, sai idan ya dakatar da kai wa al’ummo hare-hare saki duk mutanen da ya sace ba tare da ɓata lokaci ba.

Bincike ya nuna ’yan Najeriya ba su gamsu da gwamnatin Tinubu ba Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano NAJERIYA A YAU: Mene ne tasirin naɗin Mataimaka na Musamman a rayuwar jama’a?

“Idan har da gaske yana neman sulhu, to sai ya nuna a aikace, ya dakatar da hare-hare kan ƙauyuka tare da sakin duk mutanen da ke hannunsa ba tare da sharaɗi ba,” in ji Kanar Ahmed, wanda ke jaddada muhimmancin tsaron rayuka da lafiyar da kuma dukiyoyin al’umma ga gwamnatin Jihar Sakkwato.

Don haka ya, “Ba za a iya yin wata sahihiyar tattaunawar sulhu da za a yi a samu a yayin al’ummomi suke zaune cikin tsoro kuma ’yan ta’adda suke yin garkuwa da mutane.

“Matakin farko na samun zaman lafiya shi ne gina yarda ta hanyar ɗaukar ƙwararan matakai a aikace,” in ji jami’in gwmanatin.

Ya jaddada aniyar gwamnatin ga tabbatar da tsaro da zaman lafiya, amma ba za ta lamunci ta’addancibda sauran miyagun laifuka ba.

Sa’annan ya yi kira ga al’ummomi da shugabannin addini da sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin faren hula su mara wa shirye-shiryen zaman lafiya baya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Garkuwa gwamnati hare hare Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya.

Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.

Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.

“Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji shi.

Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta tallafa wa Najeriya da sabbin fasahohi domin yaƙar matsalar tsaro maimakon yin kalaman da za su iya raba kan ’yan ƙasa.

“Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance matsalolin tsaro, maimakon yin barazanar da za ta ƙara raba ƙasar,” in ji Kwankwaso.

Haka kuma, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta naɗa jakadu na musamman domin inganta hulɗar diflomasiyya da Amurka da kare muradun ƙasar a matakin duniya.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya, inda ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya dace a fifita haɗin kan ƙasa ba abin da ke raba ta ba.

“Wannan lokaci ne da ya kamata mu mayar da hankali kan abin da zai haɗa kanmu ba wanda zai raba mu ba. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida