Mutum 330 Sun Mutu Yayin da Isra’ila Ta Kai Wa Gaza Sabbin Hare-hare
Published: 18th, March 2025 GMT
Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce, “A daren yau mun koma yaƙi a Gaza.”
Hamas ta zargi Isra’ila da karya yarjejeniyar tsawon kusan wata biyu, tana mai cewa hakan na barazana ga lafiyar fursunonin da ke tsare a Gaza.
Amma Isra’ila ta ce Hamas ce ke ƙin sakin fursunonin tare da bijirewa yarjejeniyar sulhu.
A lokacin yarjejeniyar, an yi musayar wasu fursunonin Isra’ila da Falsɗinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra’ila.
Sai dai har yanzu kimanin mutum 59 daga cikin fursunonin Isra’ila suna hannun Hamas, kuma ana zargin rabinsu sun mutu.
Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta amince da harin da Isra’ila ta sake kai wa Gaza, inda ƙasashen biyu suka sha alwashin yaƙar Hamas, ‘yan tawayen Houthi na Yemen, da sauran ƙungiyoyin da suka ɗauki makamai.
Kakakin fadar White House, Karoline Leavitt, ta yi gargaɗin cewa, “Hamas da Houthi za su fuskanci sakamako mai tsanani. Duniya za ta girgiza.”
A cewar Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, aƙalla Falasɗinawa 48,577 ne suka mutu, yayin da Ofishin Yaɗa Labarai na Gaza ya ce adadin ya haura 61,700, ciki har da waɗanda ke birne a ƙarƙashin gine-ginen da aka rushe.
Yaƙin ya fara ne bayan harin da Hamas ta kai kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Isra’ilawa 1,139 tare da tsare da sama da mutum 200.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Falasɗinawa Hare Hare Isra ila yaƙi
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun daƙile harin ’yan bindiga, sun ceto mutum 25 a Zamfara
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta daƙile wani hari da ’yan bindiga suka kai wa al’ummar Kuraje da ke gefen birnin Gusau.
Wasu gungun ’yan bindiga, ɗauke da makamai ne, suka kutsa cikin ƙauyen suna harbi, lamarin da ya jefa mazauna Kuraje da maƙotan ƙauyukan cikin tashin hankali.
Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta NejaA yayin harin, sun yi awon gaba da mata 10 da yara 15.
Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce ’yan sanda sun ɗauki mataki bayan samun kiran gaggawa.
Ya ce tawagar haɗin gwiwa daga sashen Damba, Sashen Ayyuka da kuma Rundunar Tsaron Al’umma (CPG) sun isa ƙauyen cikin gaggawa.
Sun bi sahun ’yan bindigar, sannan suka yi artabu da su.
’Yan sanda sun ceto dukkanin mutum 25 ba tare da kowa ya ji rauni ba.
An kai matan da yaran zuwa Sabon Gari Damba domin kula da su, kafin su da iyalansu.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya yaba wa jarumtar jami’an da suka yi aikin, tare da tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyinsu.