DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna
Published: 19th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A karshe dai abin da wasu ke hasashen zai faru a Jihar Ribas ne ya faru inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar kuma ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa da kuma ’yan majalisar dokokin jihar.
Sai dai bayan wannan doka da shugaban kasar ya ayyana ne al’umma da dama ke ta bayyana mabanbantan ra’ayoyin kan wannan batu.
A yayin da wasu ke bayyana cewa dama tuni abin da shugaban kasar yake bukata ke nan, wasu kuwa ke bayyana cewa shugaban kasar ma ba shi da ikon dakatar da zababben gwamna.
NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa?Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan shin ko Dokar Kasa ta bai wa shugaban kasa karfin ikon dakatar da gwamnan jiha dama ’yan majalisar dokokin ta?
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dokar Dokar Ta Ɓaci siminilaye Fubara
এছাড়াও পড়ুন:
Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu
Tsoffin ma’aikatan Hukumar Shirya Jarabawar (NECO), da suka yi ritaya na neman a biya su haƙƙoƙinsu da suke bin bashi.
Shugaban ƙungiyar tsofffin ma’aikatan, Dokta Abdullahi Rotimi Williams ne ya bayyana hakan a bikin ƙaddamar da hedikwatar kungiyar a Minna, babban birnin Neja.
Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta NijeriyaShugaban ya kuma koka kan yadda gwamnatin Nijeriya ta maida ritaya abin fargaba a wurin ma’aikata saboda tarin ƙalubalen da ke biyo bayan hakan, musamman maƙalewar haƙƙoƙinsu.
“Da yawa tsoron ritaya ake yi yanzu. Don haka wannan ƙungiyar za ta taimaka wajen rage waɗannan matsalolin.
“Babban ƙalubalen da muke fuskanta shi ne na lafiya. Don haka ina roƙon shugaban hukumar da ya tabbatar cewa daga yanzu an kammala shirye-shiryen da suka kamata kafin ma’aikacin NECO ya yi ritaya.”
Ya kuma ce duk da jagororin hukumar na yanzu sun biya wasu daga cikin haƙƙoƙin nasu, ba a kai ga biyan alawus ɗin ƙarin girma ba, da na tafiye-tafiye ba.