Aminiya:
2025-11-02@21:33:17 GMT

Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos

Published: 7th, July 2025 GMT

Wata babbas bas din haya kirar Macarpollo dauke da fasinjoji  ta yi hatsari a garin Jos, hedikwatar Filato.

Motar mai daukar fasinjoji 56 ta yi hatsari ne bayan isowarta Mahadar Vom da Anguldi da ke Jos, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Hatsarin ya auku ne kimanin milomita 10 kafin motar ta isa inda za ta tsaya bayan doguwar tafiyar mai nisan kilomita.

Wakilinmu ya gano cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4 na asubahin ranar Litinin din nan, inda motar ta lalata kusan daukacin shagunan da ke wurin da ta yi hatsari.

’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a Borno Turji: Gwamnatin Sakkwato ta ba da sharadin sulhu da ’yan ta’adda

Wani mazaunin yankin da ke sana’ar sayar da kifi ya bayyana cewa ba a samu asarar rai ba, kuma mutum daya ne kadai ya samu rauni a motar.

Jami’in Wayar da Kan Jama’a na Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a Jihar Filato, Yakubu Lonsan, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kara da cewa hukumar tana yin duk abin da ya kamata domin kawar da motar da ma cunkoso a wurin da abin ya faru.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hatsari Macarpollo motar ta yi hatsari

এছাড়াও পড়ুন:

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025 Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025 Wasanni Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025? November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya
  • Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda