Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Jigawa ta Kwace Gurbatattun Kayayyaki na Miliyoyin Naira
Published: 7th, July 2025 GMT
Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Jigawa (JISEPA) ta yi kira ga al’umma da su ba da hadin kai wajen tabbatar da tsafta da kuma bayar da rahoton duk wani da ake sayarwa da ba bisa ka’ida ba, ko kuma cikin rashin tsafta.
Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Adamu Sabo ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
A cewarsa, wannan kira ya zama wajibi sakamakon nasarar da hukumar ta samu na kwace gurbatattun kayayyakin na sama da naira miliyan 14 a lokacin sintiri da binciken kayayyaki a fadin jihar daga watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2025.
Alhaji Adamu Sabo ya kara da cewa, mafi yawancin kayayyakin da aka kwace na ci ne da suka lalace, ko kuma wadanda aka adana ba bisa ka’ida ba, ko kuma suka lalace har suna barazana ga muhalli da lafiyar jama’a.
Ya bayyana cewa wann
an sintiri na tabbatar da tsafta yana cikin ayyukan hukumar domin inganta lafiyar jama’a da tabbatar da tsaron muhalli, tare da tabbatar da ka’idojin tsafta.
Sabo ya ce dukkan kayayyakin da aka kama an kaddamar da su bayan an bi dukkan matakan doka, an tantance su, sannan aka amince da lalata su bisa dokokin kiwon lafiya na jama’a.
“Wannan aikin an gudanar da shi ne bisa tsarin doka kamar yadda sashe na 5(1)(2) na Dokar Kariya ta Muhalli ta Jihar Jigawa ta shekarar 2009 (wanda aka gyara), da kuma sashe na 125(1) na Dokar Tsaron Lafiyar Jama’a ta Jihar Jigawa ta shekarar 2024 suka tanada”. In ji shi.
Ya jaddada cewa, wannan mataki rigakafi ne na kare lafiyar jama’a da tabbatar da tsaron muhalli da tsaftar Jihar Jigawa ba don kuntatawa wani ba.
Ya kara da cewa, hukumar za ta ci gaba da yin aiki tare da kungiyoyin kasuwa, ‘yan kasuwa da shugabannin al’umma domin tabbatar da cikakken bin dokokin muhalli da na lafiyar jama’a.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa ta Jihar Jigawa lafiyar jama a tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya yi gargaɗin cewa dogaro da soja kaɗai, ba tare da inganta rayuwar jama’a ba, zai ƙara haifar da rikice-rikice.
Ya ƙara da cewa ingantacce tsaro na ƙasa yana farawa ne idan gwamnati ta ƙirƙiro damarmakin samun aiki da kuma mayar da amincin jama’a ga gwamnati.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA