Harin Jirgin Yakin Sojoji Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 18 A Kasuwa
Published: 19th, March 2025 GMT
Majiyar ‘yan aware ta kasar Mali ta sanar da cewa wani hari da sojojin gwamnati su ka kai a arewacin kasar ya yi sanadiyyar kashe mutane 18 a arewacin kasar Yemen, sai dai sojojin gwamnatin ta ce, ‘yan aware ta kai wa hari.
Kungiyar Azbinawa ‘yan aware ta ce sojojin gwamnatin kasar sun kai hari ne a garin Lerneb mai nisan kilo mita 50 daga birnin Timbuktu, a ranar Litinin da ta gabata kuma bayan mutane 18 da su ka kwanta dama, wasu 7 sun jikkata.
Kungiyar ta Azbinawa ta bayyana abinda ya faru da cewa; “Dabbanci” ne irin na zamanin jahiliyya.
Sai dai sojojin gwamnatin kasar ta Mali sun wallafa a shafinsu na X cewa; sun kai harin ne akan wata tunga ta ‘yan ta’adda tare da kashe 11 daga cikinsu.
Fiye da shekaru 10 kenan kasar ta Mali tare da makwabtanta, Burkina Faso da Nijar suke fada da kungiyoyi masu dauke da makamai da su ka hada al’ka’ida da kuma “Da’esh”.
Bayan juyin mulkin da aka yi a cikin kasashen uku, da korar sojojin Faransa, kasar ta Mali ta gayyato mayakan kungiyar “Wagner” daga kasar Rasha, domin taya ta fada da masu dauke da makaman.
Sai dai a wasu lokutan ana samun kuskure irin wannan da wajen kai wa masu dauke da makamai hari, ake kai wa fararen hula.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun yi juyin mulki a Jamhuriyar Benin
Sojoji a kasar Jamhuriyar Benin sun kifar da gwamnati a wani juyin mulki da suka sanar a ranar Lahadi.
Sojojin sun bayyana ne a gidan talabijin na kasar inda suka sanar da tsige Shugaban Kasa Patrice Talon da kuma rushe duk hukumomin kasar.
Dakarun, karkashin jagorancin Laftanar Kanar Pascal Tigiri, sun rufe iyakokin kasar da rushe jam’iyyun siyasa.
Zuwa lokacin kammala wannan labarin babu labarin halin da Shugaba Talon wanda ke kan karagar mulkin tun a 2016 yake ciki.
Amma ministan harkokin kasar, Olusegun Ajadi Bakari, ya ce an samu yunkurin kifar da gwamnati, amma ana neman shawo kan lamarin.