HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano
Published: 19th, March 2025 GMT
Wata gobara da ta auku safiyar wannan Larabar ta laƙume kasuwar ’yan gwan-gwan da ke unguwar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano.
Kasuwar wadda ake kira da Kwalema tana nan a kan titin Zango, daura da gidajen man Dominion da kuma Mobil da ke makwabtaka da ofishin Hukumar WAEC.
Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen GwamnaMai magana da yawun hukumar kwana-kwana Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa jami’ansu na ci gaba da ƙoƙarin kashe gobarar da ke neman wuce gona da iri.
Sai dai ya bayyana cewa duk da bincike ya soma gudana, amma kawo yanzu ba su gano musabbabin tashin gobarar ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara Gwangwan Jihar Kano Kwalema
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ’yan bindiga 4 a Kano
An kama wasu mutum huɗu da ake zargin ’yan bindiga ne ɗauke da makamai da ake zaton bindigogi ne a tashar mota ta Ƙofar Ruwa da ke Jihar Kano.
Tashar motar, wadda ke kusa da kasuwar kayan gini ta Ƙofar Ruwa a Ƙaramar Hukumar Dala.
MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’aA cewar mazauna yankin, an kama mutanen ne lokacin da suke ƙoƙarin shiga mota domin tafiya zuwa wani waje a cikin Kano.
“Mutanen da ke tashar motar ne suka lura da makaman da suke ɗauke da su. Take suka gaggauta sanar da jami’an tsaro, waɗanda suka kama su. Su huɗu ne gaba ɗaya,” in ji Musa Balarabe, wani mazaunin yankin.
Ya ce an kama su ne da misalin ƙarfe 1 na rana.
Da farko an kai su ofishin ’yan sanda na Ƙofar Ruwa, kafin daga bisani aka mayar da su ofishin Dala.
Wani mazaunin yankin, Umar Nuhu, ya ce yana cikin shagonsa da ke Kwanar Taya, kusa da ofishin ’yan sandan, lokacin da aka kawo mutanen.
Ya ce hakan ya jawo firgici, inda mutane suka fara gudu a ko’ina.
Nuhu, ya ƙara da cewa mutane da yawa sun yi dandazo a ofishin ’yan sandan, yayin da wasu matasan ke son ɗaukar doka a hannu.
Da aka tuntuɓi kakakin ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, bai ce komai kan lamarin ba.
Ya ce har yanzu suna tattara bayanai kafin su fitar da sanarwa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sabuwar sanarwa daga rundunar ’yan sandan jihar.
Tashar Kofar Ruwa, tasha ce da ke jigilar fasinjoji zuwa jihohi irin su Katsina, Jigawa, Sakkwato, Zamfara, Kebbi, har ma da Jamhuriyar Nijar.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Jihar Kano ke fama da hare-haren ’yan bindiga, musamman a yankunan da ke da iyaka da Jihar Katsina.