Aminiya:
2025-07-07@19:27:53 GMT

Bidiyon tsiraici: Babiana ta sake jawo ce-ce-ku-ce

Published: 7th, July 2025 GMT

A ƙarshen makon da ya gabata ne fitacciyar ’yar TikTok wacce aka fi sani da Babiana ta fitar da wani sabon bidiyo tana rusa ihu tana kira ga Shugaba Bola Tinubu da wasu mawaƙan kudancin Najeriya da su shiga tsakaninta da ’yan Arewa a kan abin da tace suna yi mata na cin zarafi tun bayan bayyanar bidiyo tsiraicinta a shekarar 2024.

Babiana ta yi bidiyon ne cikin harshen Ingilishi inda ta ce ba a yi mata adalci a Arewa kuma ana barazana da rayuwarta.

Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos

Ta bayyana cewa tsawon shekara ɗaya ta yi tana raɓe-raɓe saboda ba ta son maganganun da mutane ke mata tun bayan bayyanar bidiyon tsiraicin nata a soshiyal midiya.

“Ina cikin halin ƙunci da damuwa, ’yan Kudu ku taimaka min Musulman Arewa na son ganin bayana” a cewar Babiana cikin harshen Ingilishi.

Yar TikTok ɗin ta ƙara bayyana cewa tun bayan ɓullar bidiyon tsiraicin nata ta shiga cikin damuwa inda kusan kullum cikin kuka take kwana, kuma har yanzu ’yan Arewa suna mata barazana da bidiyon.

Sabon bidiyo nata ya tayar ƙura, inda wasu ke ganin kalaman nata ba su kamata ba, kuma babu adalci a ciki, kuma ba ta ɗauko hanyar shawo kan matsalar ba.

Nasiru Salisu Zango, sharhi ya yi akan lamarin inda ya ce “ko da yake a cikin bidiyon Babiana ta yi maganganu na ɗora alhaki kan al’ummar Arewa Musulmai wanda hakan rashin adalci ne, amma fa duk da haka akwai buƙatar jan hankalin masu yaɗa bidiyon kan suji tsoron Allah.”

Ya ƙara da cewa “ya kamata a tausaya mata tun kafin ta faɗa wani yanayin na daban, mun sani tana da ’ya’ya da ’yan uwa da wannan yaɗa bidiyon zai iya rikita wa rayuwa.”

Shi kuwa Bilyaminu Ayuba, cewa ya yi ai dama alhaki kuikuyo ne kuma Babiana ba ta ɗauko hanyar da ya kamata ba wajen gyaran wannan matsalar duk da ya bayyana cewa abin da ake matan bai dace ba.

“ A ganina Babiana ba ta ɗauko hanyar gyara matsalar ba saboda shi mutumci madara ne, idan ya zube shi ke nan kuma har yanzu tana son shisshigi da aibanta mutane shi ya sa kullum za a dinga sukar ta da wannan bidiyon nata na marke.

“Idan har tana son zaman lafiya a rayuwarta, to dole ta daina jifa da shisshigi wa mutane, wannan shi ne. Allah Ya sa mu dace.”

Jamilu Sani a nasa ɓangaren cewa ya yi “a cikin lamarinki akwai wa’azi. A baya kece mai yaɗa bidiyon waɗansu idan sun yi irin wannan abin da kika kira kuskure, yau sai Allah Ya kama ki domin ki ji yadda kika jiyar da ’yan uwanki mata marasa tarbiyya da tunanin gobe.”

Ya ƙara da yin kira ga sauran mutane cewa Babiana da ire-irensu marasa “hangen nesa, sun yi aiki marar kyau a ɓoye. Sun yi wa kansu bidiyo, idan suka tuba , tuba na gaske, sai Allah Ya yafe musu.”

Hafsat Muhammed cewa ta yi, “Ita har ta manta duk abubuwan da ta yi wa mutane, kuma har yau ba ta nemi yafiyarsu ba har tana ma kanta kirari da ‘Queen of Update.’”

Abdulwahab Sa’id Ahmad a shafinsa na Facebook wallafawa ya yi cewa: “Wanda yake da cutar Depression ba shi yake ganewa ba sai dai a gane masa.

“Mahaukaci bai san yana hauka ba sai dai a ba shi labari bayan ya warke

“Ki bar nunawa cewa Musulmi sun yi watsi da ke da ’yan Arewa, ke ce ki ka zaɓi ki zauna a yadda ki ke.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Rasha Tana Ci Gaba Da Karya Kadarin Kasashen Turai A Yakin Da Suke Yi A Ukraine  


Shugaban kasar Rasha ya aike da sako mai zafi wa kasashen Yammacin Turai da suke tallafawa Ukraine

A daidai lokacin da yakin Rasha da Ukraine yake ci gaba da ruruwa, kuma har yanzu an gagara cimma tsagaita wuta. Sabbin abubuwan da suka faru a fagen sojan Rasha sun hada da ma’aikatar tsaron kasar da ta sanar da cewa sojojin kasar sun ‘yantar da garuruwan Poddubnoye na Donetsk People’s Republic da Sobolevka a yankin Kharkiv.

Sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta bayyana cewa: Sojojin kasar Rasha sun ci gaba da zurfafa kai hare-hare kan makiya, inda suka yi ta janyo hasarar bil’adama da na dukiya kan sojojin kasar Ukraine a yankuna da dama na jamhuriyar Donetsk People’s Republic da yankin Dnipropetrovsk. Sojojin Ukraine sun yi hasarar ma’aikata fiye da 390, da motocin yaki masu sulke, da kuma wasu manyan bindigogin fage.

A cikin iska … Jiragen saman Rasha na aiki da dabara sun lalata ababen more rayuwa na filayen jiragen sama na soji, da masana’antar kere-kere, ma’ajiyar ajiyar jirage marasa matuka ciki, da tashar mai da rusa sansanonin sojoji, sannan suka kakkabo bama-bamai na iska guda shida da jiragen sama 298.


সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Reuters: Amurka Tana Da Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza
  • Firaministan Kasar Sin: Kasarsa Ta Kimtsa Tsaf Wajen Inganta Aikin BRI Da Bunkasa Kasuwanci Da Zuba Jari Tare Da Habasha
  • Kasar Rasha Tana Ci Gaba Da Karya Kadarin Kasashen Turai A Yakin Da Suke Yi A Ukraine  
  • Ƴan Arewa Za Su Yi Murna Idan Na Zama Shugaban Ƙasa — Peter Obi
  • Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Tunisiya Da Ci 3-0 A Moroko
  •  Togo: An Yi Kiran Sake Yin Wata Sabuwar Zanga-zanagr Kin Jinin Gwamnati
  • Gobe Za A Fara Wasannin Kofin Afirka Na Mata
  • Gonakin Koko: Mata sun yi barazanar zanga-zanga tsirara a Kuros Riba
  • Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A Zaɓen 2027 Ba – NNPP