Mutane 21 Suka Mutu A Hatsarin Mota A Hanyar Zaria Zuwa Kano
Published: 7th, July 2025 GMT
Mummunan lamari ya faru ne a lokacin da wata mota kirar bas ta kasuwanci da wata babbar mota ta yi taho-mu-gama da tare da daukar rayukan mutane 21 a hanyar Zariya zuwa Kano.
Hadarin ya afku ne a Kasuwar Dogo, Dakatsale, wanda ya hada da wata motar kasuwanci kirar Toyota Hiace da wata tirela ta DAF.
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa direban motar bas din ya saba ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa, lamarin da ya kai ga yin karo da babbar motar da ke zuwa.
Hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji 21 nan take, wadanda suka hada da manya maza 19 da manya mata 2, yayin da wasu uku suka samu raunuka, kuma an kai musu daukin gaggawa.
Jami’an FRSC tare da sauran kungiyoyin bayar da agajin gaggawa sun isa wurin domin gudanar da aikin ceto tare da kwashe tarkacen motocin, wanda hakan ya baiwa ababen hawa damar ci gaba da amfani da hanyar.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban Rundunar FRSC, Marshal Shehu Mohammed, ya bayyana matukar alhininsa game da asarar rayuka da aka yi, ya kuma jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.
Ya kuma tabbatar da cewa, ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike domin gano cikakken al’amuran da suka faru a hatsarin.
“Wannan mummunan bala’i kuma wani abin tunawa ne mai raɗaɗi na mummunan sakamakon rashin biyayya ga dokokin hanya,” in ji shi.
“Tuƙi gangaci da wuce gona da iri sune manyan abubuwan da ke ba da gudummawa ga irin waɗannan bala’o’in da za a iya gujewa a kan hanyoyinmu.”
Rundunar ta Corps Marshal ta bukaci dukkan direbobi musamman masu sana’ar tuki da su bi ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa.
Ya kuma jaddada cewa za a kara kaimi wajen tabbatar da tsaro da wayar da kan jama’a domin hana ci gaba da asarar rayuka.
Hukumar ta FRSC ta yi kira ga masu amfani da hanyar da su kai rahoton hatsarita hanyar kiran lambar kyauta 122, ko kuma a tuntubi duk wata tawagar sintiri ta FRSC.
An ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a asibitin Nasarawa dake Kano, inda ake jiran tantancewa da kuma mikawa iyalansu.
Rel/Khadijah Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Hatsari
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙwallo ta kashe ɗan wasan Cricket
Wani haziƙin matashin ɗan wasan Cricket mai shekara 17 ɗan asalin ƙasar Australiya ya mutu a yau Alhamis bayan ƙwallo ta buge shi a lokacin wasa.
Ƙwallon ta bugi, Ben Austin a wuyansa ne duk da cewa yana sanye da hular kariyar kai (Helmet) a lokacin da yake ƙoƙarin kare ƙwallon da aka bugo.
Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a Ekiti Gobara ta tashi a babban kanti a AbujaNan take aka garzaya da shi asibiti cikin mawuyacin hali, daga bisani rai ya yi halinsa.
“Mun yi matuƙar baƙin ciki da rasuwar haziƙi Ben ɗinmu, wanda ya mutu da safiyar yau Alhamis,” in ji mahaifinsa Jace Austin a cikin wata sanarwa.
A cewar jaridar ABC News, matashin ɗan wasan bai sanya rigar da ke kare wuyansa ba, hakan ne ya sa ƙwallon ta dufafe shi.
Austin ya kasance ƙwararren mai buga ƙwallo, wanda ƙungiyarsa ta Ferntree Gully Cricket Club ta ɗauke shi a matsayin “ɗan wasan Cricket mai hazaka, babban jagora kuma matashi mai ban mamaki”.
‘Yan wasa daga ƙungiyoyin biyu na India da Australia a ɓangaren mata da ke buga wasan Cricket na duniya sun sanya baƙaƙen kambu domin alhinin mutuwarsa.
Yau dai kimanin shekaru 11 rabon da wani ɗan wasan Cricket ya mutu a lokacin wasa, tun bayan da shahararren ɗan wasan nan ɗan asalin ƙasar Australia Test Phillip Hughes ya mutu a 2014.