Ba tarbiyya nake koyarwa ba — Sadiq Sani Sadiq
Published: 19th, March 2025 GMT
Fitaccen jarumi a Masana’antar Kannywood Sadik Sani Sadik ya ce shi ba fadakarwa yake yi a fim ba, inda ya ce neman kuɗi kawai yake yi.
Jarumin ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Gidan Rediyon Freedom, inda a ciki yake cewa ba tarbiyya yake koyarwa ba, ballantana a ce yana bata tarbiyyar.
Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a RibasA cewarsa, “Ni ban ce ina fadakarwa ba.
“Tarbiyya ana ba yaro daga gida ne, fadawarka kuma malamai ne ke yi. Ni ba mai fadakarwa ba ne. Ni mai neman kudi ne.
“Shi fim ba ya da yare, ba ya da addini, saboda haka ya danganta da yanayin da za ka gudanar da fim dinka.
“Idan danka ya kalli fim dina, tarbiyyarsa ta tabu, ba daga ni ba ne, daga kai ne. Idan ma danka bai kalli fim din Hausa ba, zai kalli na Indiya da wakokin Turawa da ake rungume-rungume.
“Ni kuma a fim din Hausa idan na taba hannun mace ya zama abin magana, ban isa ba wallahi.”
Game da mata sun fi maza samun kudi, sai ya ce, “Wasu matan sun fi wasu mazan kudi.
“Kudi ai sirri ne ba wai ka ga mutum ya hau motoci ko ya sanya gwala-gwalai ba ne.
“Ya danganta ne, wani idan yana da dubu daya sai ka gane, wani kuma yana da miliyan daya, amma ba za ka gane ba.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu mutum biyar sakamakon haɗura uku da suka auku a jihar.
Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce hatsrin farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Badawa Layin Day by Day ca Ƙaramar Hukumar Nassarawa.
Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin Jirgin sojin sama ya yi hatsari a NejaLamarin ya faru ne a wani gida mai faɗin kafa 25 da 20 wanda ya kama da wuta.
Ma’aikatan kashe gobara sun ceto wata yarinya mai shekara 10 daga a cikin gidan, amma daga baya ta rasu a asibiti.
An bai wa iyayenta gawarta.
Hatsari na biyu ya faru ne a Ƙauyen Badume Kanawa da ke Karamar Hukumar Bichi.
Wani mutum mai shekara 65, Sa’idu Gada, yana aiki a cikin rijiya lokacin da igiyar da ta ke riƙe da shi ta tsinke, ya faɗa ciki.
Ɗansa mai shekara 20, Sani Isyaku, ya shiga rijiya domin ceto shi, shi ma ya maƙale.
Wani mutum na uku, Yakubu Abdullahi mai shekara 60, ya shiga domin taimakonsu, shi ma daga bisani ya faɗa cikin rijiyar.
Ma’aikatan hukumar sun fito da su daga rijiyar, amma sun riga sun rasu.
An miƙa wa ’yan sandan Badume gawarwakinsu.
A wani lamari na daban kuma, wani yaro mai shekara 10, Hassan Iliyasu Haruna, ya zame tare da faɗa wa rijiya a Ƙaramar Hukumar Danbatta.
Ma’aikatan hukumar kashe gobara sun ceto shi, amma daga baya ya rasu.
An miƙa wa mahaifinsa gawar yaron.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Kano, Sani Anas, ya ja hankalin jama’a da su daina shiga rijiya domin ceto mutane, domin a cewarsa hakan na da hatsari.