2025-07-07@22:16:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4531
«Festus Keyamo»:
Gwamna Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutane 48,000 domin jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙara ƙarfafa matakan kiwon lafiya a matakin farko a fadin Jihar Yobe. Buni ya bayyana shirin fara samar da daidaito a bangaren kiwon lafiya wanda zai samar da inshorar lafiya ga mata masu rauni da yara ‘yan...
Gwamna Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutane 48,000 domin jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙara ƙarfafa matakan kiwon lafiya a matakin farko a fadin Jihar Yobe. Buni ya bayyana shirin fara samar da daidaito a bangaren kiwon lafiya wanda zai samar da inshorar lafiya ga mata masu rauni da yara ‘yan...
NiMet ta ce duk wanda ke zaune a wuraren da ruwa ke taruwa ko wuraren da aka bayyana yana da haɗari da su koma wuri mafi aminci. An kuma shawarci jama’a da su tanadi kayan gaggawa kamar abinci mai yawa da ruwa da kayan taimakon gaggawa da fitila da na’urar adana lantarki ta ‘power bank’....
An gudanar da taron kafa kungiyar masana masu binciken sararin samaniya mai zurfi ta kasa da kasa wato IDSEA a birnin Hefei dake lardin Anhui, yau Litinin. Wannan ita ce kungiyar masana kimiyya da fasaha ta kasa da kasa ta farko da kasar Sin ta kafa a fannin binciken sararin samaniya mai zurfi. A cikin...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a birnin Yangquan na lardin Shanxi a yau Litinin. Shugaban ya ziyarci dandalin da aka kebe domin tunawa da katafaren gangamin soji na yaki da harin Japan, inda ya gabatar da furanni ga wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin. Ya kuma ziyarci babban dakin tunawa da gangamin....
(ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya. Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai...
(ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya. Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai...
Wannan lamari ya buɗe sabon shafi a siyasar ƙasar nan, inda ƴan adawa suke ci gaba da cewa zuwan sabuwar jam’iyyar wani sauyi ne da za a samu a cikin ƙasar. Wani mai sharhi a kan siyasa, Sani Kabo, ya bayyana abin da ya samu shafin yanar gizon jam’iyyar a matsayin wata ƴar manuniya ga...
Kananan yara uku sun rasu yayin da wasu da shidan ke kwance a asibiti sakamakon sake bullar cutar nan ta mashako a garin Zariya da ke Jihar Kaduna. Wani mazaunin unguwar Kwarbai a yankin na Zariya, Mallam Bashir Magaji wanda ya rasa ’yarsa sakamakon barkewar cutar wadda a turance ake kira Diphtheria, ya bayyana yadda...
Kasar Sin ta gudanar da bikin cika shekaru 88, da dukkan al’ummar kasar ta fara yakin kin jinin harin sojojin Japan a yau Litinin. Inda a wani bangare na bikin aka kaddamar da wani baje koli mai taken “Domin ‘yantar da kasa da zaman lafiyar duniya”. An gudanar da bikin tare da baje kolin ne...
Rahotanni da suke fitowa daga kasar ta Kenya sun ce tun safiyar yau Litinin ne ‘yan sanda su ka rufe muhimman hanyoyin da su ka nufi tsakiyar babban birnin kasar Nairobi da kuma muhimman cibiyoyin kasuwanci. Kafafen watsa labarun kasar ta Kenya sun ce da akwai jami’an ‘yansanda masu yawa da aka girke su a...
Saboda matsin lamba na doka da kuma la’akari da mahimman batutuwan siyasa, ya zama dole Gwamnatin Jihar Bauchi ta dakatar da duk wani ci gaba na aikin kwamitin da aka kafa a ranar 4 ga Yuli 2025 domin duba yiwuwar ƙirƙirar sabbin masarautu ko sauye-sauye ga tsarin majalisun gargajiya—musamman a yankunan da har yanzu ke...
Ma’aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta ware dala miliyan 130 a kasafin kudinta na 2026 karkashin Yaƙi da ISIS da Kudin Kayan Aiki (CTEF) don taimaka wa kungiyoyi masu dauke da makamai a Syria, cikin su har da SDF da YPG ta mamaye. Wannan dai na zuwa ne a yayin da Siriya ke ci gaba da...
A ƙarshe, lauyoyin Majalisar sun ja hankalin lauyoyin Sanata Akpoti-Uduaghan da su yi taka-tsantsan don kauce wa yi wa kundin tsarin mulki kutse ko sanya rikici a majalisa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Rahotanni sun bayyana cewa mazauna wasu jihohin Nijeriya uku na cikin shirin ko-ta-kwana, sakamakon ƙaruwar fargabar samun ambaliya saboda yiyuwar sakin ruwan Madatsar Lagdo ta Kamaru. A cewar wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa, jihohin da mazauna ke cikin zaman ɗar-ɗar sun haɗar da Benuwe da Edo da kuma Bayelsa, waɗanda tuni suka fara...
An kashe mutane tara tare da jikkata wasu huɗu a wani da mayakan Boko Haram suka kai yankin a Malam Fatori da ke Jihar Borno. Gwamna Babagana Zulum, wanda baya kasar a halin yanzu, ya tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Sugun Mai Mele, domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa da kuma tantance...
Wani sojan ko-ta-kwana na Isra’ila ya kashe kansa sakamakon tsananin firgici da damuwar da ya shiga a yaƙin Gaza wanda Isra’ila ke aikata kisan-kiyashi. Shafin labarai na Isra’ila, Walla, ya bayyana cewa Daniel Adri mai shekaru 24, wanda ya yi aiki a Gaza da Lebanon, ya kashe kansa bayan doguwar gwagwarmayar da ya yi da...
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari da safiyar Litinin a unguwar Ogaminana da ke ƙaramar hukumar Adavi a Jihar Kogi, inda suka kashe wani Soja ɗaya da aka tura domin bayar da kariya ga ma’aikatan kamfanin gine-gine. Wata majiya daga yankin ta shaida wa LEADERSHIP cewa maharan sun mamaye...
Shugaban kasar Rasha ya aike da sako mai zafi wa kasashen Yammacin Turai da suke tallafawa Ukraine A daidai lokacin da yakin Rasha da Ukraine yake ci gaba da ruruwa, kuma har yanzu an gagara cimma tsagaita wuta. Sabbin abubuwan da suka faru a fagen sojan Rasha sun hada da ma’aikatar tsaron kasar da ta...
Sojojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya sun kai hare-hare kan tashar jiragen ruwa na Hodeidah a kasar Yemen Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan tashar ruwan Hodeidah da ke yammacin kasar Yemen, biyo bayan barazanar da sojojin kasar suka yi a yammacin jiya Lahadi. Majiyar Yemen ta fada a yammacin jiya Lahadi cewa: An...
Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun yi Allah wadai da hare-haren zaluncin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yemen Kungiyar Jihadin-Islami ta Falasdinawa da sauran kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci na Falasdinu sun yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan tashar jirgin Ruwan Hodeida na kasar Yemen, tare da jaddada...
Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya rasu, yana da shekara 90 a duniya. Kakakin iyalan basaraken ne ya tabbatar da mutuwarsa da safiyar yau Litinin cikin wani saƙo da ya aike wa manema labarai. Kwanaki biyu da suka gabata ne basaraken ya gudanar da bikin cikarsa shekara 90 a duniya a wani ƙasaitaccen biki...
An kashe mutane tara tare da jikkata wasu huɗu a wani da mayakan Boko Haram suka kai yankin a Malam Fatori da ke Jihar Borno. Gwamna Babagana Zulum, wanda baya kasar a halin yanzu, ya tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Sugun Mai Mele, domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa da kuma tantance...
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce an samar da isassun matakan tsaro domin kawar da wasu gungun miyagu da ke aikata munanan laifuka a jihar. AbdulRazaq ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana wa masu ruwa da tsaki daga yankin Lafiagi na jihar Kwara ta Arewa kan dimbin kokarin gwamnatin jihar a...
Wani malamin addinin musulunci a jihar Zamfara, Sheikh Mohammed Tukur Sani Jangebe, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara da su gaggauta gudanar da kananan gyare-gyare daga mahadar Maru –Mayanchi – Maradun, da ke kan hanyar zuwa wani yanki na karamar hukumar Talata Mafara. Ya ce mummunan yanayin hanyar yana ci...
A ƙarshe, Farfesa Pate ya yabawa gwamnatin tarayya bisa gina sabbin gine-gine a jami’ar kamar ginin Majalisar Jami’a, katangar jami’a, da ɗakunan kwana. Ya bayyana cewa dalibai 6,870 ne suka kammala karatu, ciki har da 91 da suka samu First Class da kuma 16 da suka kammala karatun digiri na PhD. Haka kuma, jami’ar ta...
Allah Ya yi wa Sarkin Ibadan, waro Olubadan, Oba Owolabi Olakulehin, rasuwa. Shaidu sun bayyana cewa Oba Owolabi Olakulehin ya koma ga Mahaliccinsa ne a safiyar ranar Litinin ɗin, 7 ga watan Yuli, 2025. Ya rasu ne yana da shekaru 90 a duniya.
Shugaban Kungiyar Harka Islamia a tarayyar Najeriya Sheikh Irahim Zakzaky ya taya mutanen kasar murna saboda nasarar da suka samu kan HKI da kuma Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan da ya gabata. Ya ce wannan nasarar bata takaita da mutanen kasar Iran kadai ba , hada har da al-ummar Musulmi da kuma...
Miliyoyin yan Najeriya ne suka gudanar da tattakin Ashoora a birne daban daban a kasar a jiya Lahadi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, da farko ya nakalto daruwan da suka fito tattakin na Ashoora a Abuja babban birnin kasar a safiyar jiya Lahadi. A wannan karon dai masu tattakin Ashoora a Abuja sun...
Kasar China ta maida martani ga takunkuman tattalin arziki na wasu kayakin kiwon lafiya wadanda tarayyar Turai da dorta maya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar kasar ta Chaina na fadar haka ta kuma kara da cewa gwargwadon takunkuman da suka dorawa kasar gwargwadon maida martanin kasar ta China. Labarin ya...
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ƙalubalanci jagoran ’yan bindiga Bello Turji, wanda ke neman sulhu, da cewa idan da gaske yake yi, to ya sako duk mutanen da ya yi garkuwa da su, ya daina kai hare-hare, kafin ta zauna da shi. Mashawarci na musamman ga gwamnan Sakkwato a kan sha’anin tsaro, Kanar Ahmed Usman ne...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Zaɓaɓɓun shugabannin gwamnati sukan naɗa wasu muƙarrabai don su taya su sauke nauyin da aka ɗora musu. Wasu na zargin naɗin ba ya rasa nasaba da sakayya ga irin rawar ga waɗanda aka naɗa saboda rawar da suka taka yayin yaƙin neman zabe. Shin irin waɗannan nade-naɗe na...
Tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Nijeriya ta fara gasar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasashen Afirika da kafar dama, bayan lallasa ƙasar Tunisia da ci 3-0 a wasan farko da suka buga yau Lahadi a filin wasa na Prince Moulay Abdellah. Asisat Oshoala da Rinsola Babajide da Chinwendy Ihezuo ne suka jefa kwallayen da suka...
Wani bincike da Cibiyar Bincike ta Africa Polling Institute (API), ta gudanar ya nuna cewa yawancin ’yan Najeriya ba su da ƙwarin gwiwa game da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Majalisar Dokoki da kuma ɓangaren shari’a. An bayyana sakamakon Binciken Haɗin Kan Al’ummar Najeriya na 2025, a wani taron ƙasa da aka gudanar a Abuja....

Mataimakin Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Sabbin Fasahohin Kimiyya A Fannin Aikin Gona Da Kiwon Lafiya
Mataimakin firaministan kasar Sin Liu Guozhong, ya yi kira da a gaggauta samar da sabbin fasahohin kimiyya a fannonin aikin gona da kiwon lafiya, da karfafa cin gashin kan fasahar kirkire-kirkiren magunguna da na’urorin likitanci. Liu, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne yayin ziyarar bincike...
“Na yi Allah- wadai da amfani da madafun iko da tsara sakamakon zabe kafin zabe ta hanyar amfani da karfin mulki da hukumomin gwamnati.” “Wajibi ne Hukumar Zabe ta samu hanyoyin magance wadannan matsalolin a wajen jefa kuri’a maimakon neman hakki a bangaren shari’a wanda daga karshe kotu za ta sanya wasu dubaru ta kori...
Elon Musk, wanda ya taɓa zama mashawarcin Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna America Party. Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (Twitter), makonni bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninsa da Shugaban Amurka. Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya Mutum 21...
Sanatan ya bayyana cewa gwamnonin yankin na farko sun ba da gagarumar gudunmuwa wajen jagorantar hadin kai wajen cimma muradun yankin daga kan ikon sarrafa albarkatun kasa zuwa matsalolin muhalli da sauransu. A kan wannan ya yi kira ga gwamnoni.masu ci a yanzu da su ci gaba da wannan al’adar, kuma su kara kokari kan...
Masanin Kenya kan huldar kasa da kasa mai suna Cavince Adhere, ya bayyana a yayin zantawarsa da dan jarida na kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan cewa, a matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa ya jaddada daidaito da samun albarkatu, inda hakan ya samu...
Labarin da dan jarida ya samu daga ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin a yau Lahadi ya nuna cewa, a kwanan baya kasashen Sin da Myanmar da Thailand sun gudanar da taron ministoci karo na biyu don yaki da laifukan zambar da ake aikatawa ta hanyar sadarwar waya. A gun taron, sassan da abin ya...
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci dakarun sojin Najeriya da su murƙushe ’yan ta’adda, masu tada ƙayar baya, da ’yan awaren Biyafara da ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. Yayin bikin Ranar Sojoji ta 2025 da ya gudana a Jihar Kaduna, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci Shugaba Tinubu. Mutum 21...
Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), reshen jihar ce ta tabbatar aukuwar hatsarin. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle. Zulum ya musanta...
Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano, kamar yadda Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle. Zulum ya musanta shirin ficewa daga...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa zai bar jam’iyyar APC zuwa ADC tare da wasu gwamnoni biyar. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya, ya fitar, Zulum ya ce wannan labari ƙarya ne, kuma wasu ne kawai ke ƙirƙirarsa domin cimma...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gargaɗi sarakunan gargajiya a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar kan zargin hannu a mamaye hanyoyin kiwo da filayen kiwo, abin da ke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma. Gwamnan ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu sarakuna na karɓar cin hanci suna kuma ba da damar...

Taron Ashura Ya Zama Lamari Mafi Girma Da Cinkoson Jama’a, Inda Masu Ziyara Daga Sassan Duniya Suka Isa Karbala
Gangamin Ashura ya zama lamarin mafi girma da cunkoson jama’a inda tattakiin Tuwairij yake gudana tare da faɗaɗa da ba a taɓa ganin irinsa ba Tattakin Tuwairij na bana zuwa birnin Karbala na fuskantar hallara da cunkoson jama’a da ba a taba ganin irinsa ba, inda dimbin masu ziyara daga sassan duniya ke tururuwa zuwa...
An sake gudanar da wani sabuwar zanga-zanga a manyan biranen duniya domin neman kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza A jiya asabar ne aka sake gudanar da wata sabuwar zanga-zanga a kasashe da dama na duniya domin nuna adawa da hare-haren da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ke ci gaba da kai wa kan...
Mataimakin shugaban kasar Iran na Farko ya ce; Al’ummar Imam Husaini a Iran ba za su bari makiya su cimma mummunan burinsu ba Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran na farko Muhammad Reza Aref ya rubuta a cikin wata wasika cewa: Domin kare martabar Iran da kasar al’ummar Imam Husaini a Iran da zuciya daya...
Babban Mufti na masarautar Oman ya yi kakkausar suka kan kasashen da ke neman kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya bayyana mamakinsa kan yadda wasu kasashe ke son kulla alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, wata kasa ‘yar mamaya maras tushe. A cikin wani bayani...