Reuters: Amurka Tana Da Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza
Published: 7th, July 2025 GMT
Kamfanin dillancin labarun “Reutres” ya bayyana cewa; Cibiyar da take tafiyar da ayyukan agaji a Gaza, wacce Amurka ta kafa ta, ta bayar da wata shawarar da take cewa; a kafa wa mutanen Gaza hemomi na wucin gadi da za su zama masomin yin hijirarsu zuwa wani wuri daban, a cikin yankin ko a wejensa.
Rahoton kamfanin dillancin labarun na Reuters ya ambato wata majiya mai karfi tana cewa; An gabatarwa da shugaban kasar Amurka shawarar tilastawa mutanen Gaza yin hijira, kuma a cikin kwanakin nan an tatauna wannan batu a fadar mulkin Amurka ta “White House.
Har ila yau rahoton ya kunshi cewa,tun daga watan Febrairu cibiyar ta fara kokarin tara kudaden da za su kai dalar Amurka biliyan 1 domin aiwatar da Shirin hijirar mutanen Gaza a cikin yankin ko kuma zuwa wajensa, da kuma kwace makaman da suke a hannun ‘yan gwagwarmaya.
A karkashin wannan Shirin da akwai matakai guda uku; Na farko shi ne bayar da kayan agaji. Na biyu shi ne gina hemomi na tsugunar da Falasdinawa a cikinsu. Na uku shi ne fitar da mutanen Gaza zuwa hijira ta dole, wacce babu dadowa.
A fili yake cewa a cikin matakin farko da har yanzu ake cikinsa, wurin da aka kira na raba kayan agaji, ba komai ba ne,sai tarko na kashe Faladinawa. Duk wanda ya je domin ya karbi kayan agaji, to ya zama abin farautar ‘yan sahayoniya.
Masu kula da wadannan cibiyoyin na agaji da aka kafa kuwa su ne; HKI da wata rundunar sojojin ‘yan ina da yaki ta Amurka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB, a wani samame da ta kai a yankin kudu maso gabashin ƙasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito wata majiya daga hedikwatar rundunar sojin tana cewa an cafke Gentle de Yahoo ne yayin farmakin da sojojin suka kai a ranar Lahadi kan sansanonin ’yan ƙungiyar a cikin wani dajin da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo.
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a RibasMajiyar ta ce a yayin cafke jagoran na IPOB, an kuma ƙwato makamai da dama daga hannunsa, ciki har da bindigogi kirar Turai, harsasai, kakin sojoji da na ’yan sanda.
“Cafke wannan kwamanda babban ci gaba ne wajen murƙushe ayyukan ta’addanci da ƙungiyar IPOB ke aikatawa, musamman a yankunan da suke hana zaman lafiya,” in ji majiyar.
Kungiyar IPOB, wacce ke fafutukar ballewa daga Najeriya don kafa ƙasar Biyafara, ta kasance a gaba-gaba wajen aikata hare-hare da ta da tarzoma a jihohin kudu maso gabas, musamman ta hannun sashen rundunar da suka kafa da kansu mai suna Eastern Security Network (ESN).
Ana dai zargin cewa Eze yana ɗaya daga cikin jagororin da ke tsara harin kwantan bauna, da hana zirga-zirga a wasu sassan yankin, wanda hakan ya jefa al’umma cikin fargaba da zaman ɗar-ɗar.
Wannan nasara na zuwa ne bayan makonni kaɗan da wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa Simon Ekpa, wani babban jigo a ƙungiyar IPOB, hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari kan laifukan da suka shafi ta’addanci da tayar da zaune tsaye.
Masu sharhi na ganin cewa cafke Gentle de Yahoo wata alama ce da ke nuna cewa ana shirin ragargaza ƙungiyar IPOB gaba ɗaya, duk da cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman ganin cewa wasu sassan yankin na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.