Gwamnatin Kasar Iran Ta Yaba Da Kungiyar BRICS Saboda Yin Tir Da HKI A Yakin Kwanaki 12
Published: 7th, July 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran wanda yake halattan taron kungiyar raya tattalin arziki ta Bricks ya yabawa kungiyar kan yin tir da Amurka da kuma HKI kan keta hurumin kasar da yaki na kwanaki 12 da kuma da kuma kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar ta zaman lafiya wadanda suke Fordo Natanz ta kuma Esfahan.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalti ministan yana fadar haka a taron kungiyar karo 17 wanda ke gudana a hilin yanzu a birnin Rio De jenero na kasar Brazil.
A ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata ne jiragen yaki na HKI suka kutsa cikin Iran inda suka kashe manya-manyan kwamandocin sojojin kasar da kuma masana fasahar Nukliyar kasar ga shahada.
Bayan haka sojojin yahudawan sun kai hare-hare kan tashar talabijin ta “Khabar” na harshen farisanci a hukumar tashoshin radio da talabijin na kasar.
Banda haka jiragen yakin Amurka B-2 sun kai hare0hare kan cibiyoyin Nukliyar kasar guda ukku.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya ta yankin Asiya da na tekun Pasifik.
Duk a wajen taron, yayin wani bikin mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanar da shi a birnin Shenzhen na kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2026. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA