Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Lardin Hodeidah Na Kasar Yemen
Published: 7th, July 2025 GMT
Sojojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya sun kai hare-hare kan tashar jiragen ruwa na Hodeidah a kasar Yemen
Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan tashar ruwan Hodeidah da ke yammacin kasar Yemen, biyo bayan barazanar da sojojin kasar suka yi a yammacin jiya Lahadi.
Majiyar Yemen ta fada a yammacin jiya Lahadi cewa: An ji karar fashewar abubuwa masu yawa a tashar jiragen ruwa na Hodeida, sakamakon farmakin da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a yankin.
A cewar majiyoyin cikin gidan Yemen, sama da fashe fashe 20 ne aka samu a Hodeidah sakamakon hare-haren da jiragen saman yakin Isra’ila suka kai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin HKI Kimani 40 Ne Suka Halaka Ko Suka Jikata A Jiya Jumma’a A Yankin Shuja’iyya Na Birnin Gaza
Kungiyar Falasdinawa ta Jihadul Islami a Gaza, ta bada sanarwan halaka ko jikatar sojojin yahudawan Sahyoniyya 40 a gaza a wani tarko mai sarkakiyan da suka dana masu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Saraya Qudus” reshen soje na kungiyar Jihadul Islamim yana fadar haka a jiya Jumma’a.
Daya daga cikin kwamnadojin dakarun ya bayyana cewa da farko halakar yahudawan ta faru ne a garin Gaza a kuma unguwar shuja’iyya. Inda da farko suka halaka sojojin yahudawa kimani 10 a cikin wani ginin da suka shiga cikinsa tare da amfani da makamai mai linzami, sannan a wani gidan
Sannan waso sojojin kimani 20 sun halaka ko sun ji rauni a lokacin dakarun suka yi am,fani da makamin TBG wanda yake watsa isakar gas da ruwa da kuma gari a inda ya fashe don kona jikin wadanda ya fashe a cikinsu.
Na uku kuma sun tana nakiyoyi masu karfi kan tankar yaki dauke da akalla sojojin yahudawa 6 suka kone .
Labarin ya kara da cewa sojojin makiya a irin wannan halin sun kasa daukar wani mataki in banda gudu daga wurin. Daga karshe ba abinda zaka gani sai gawakin sojoji a waste a yankin.