Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari da safiyar Litinin a unguwar Ogaminana da ke ƙaramar hukumar Adavi a Jihar Kogi, inda suka kashe wani Soja ɗaya da aka tura domin bayar da kariya ga ma’aikatan kamfanin gine-gine.

Wata majiya daga yankin ta shaida wa LEADERSHIP cewa maharan sun mamaye wurin aikin ne da safe, inda suka yi awon gaba da wani ɗan ƙasar China da ke aiki a wurin.

An bayyana cewa bayan harin, maharan sun ajiye motarsu a kusa da tashar watsa shirye-shiryen Radio Kogi da ke Otite, da nisan ‘yan mitoci kaɗan daga inda suka sace ɗan Chinan.

CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara Kuzari Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China

Majiyar ta ce haɗin gwuiwar jami’an Soja, da ‘yansanda, da masu farauta da ‘yan bijilanti sun bi sawun maharan cikin dazuka, lamarin da ya tilasta su bar ɗan ƙasar China da suka sace. “Har yanzu jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a dazukan yankin don kama waɗanda suka aikata wannan aika-aika,” in ji ta.

Kakakin Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Kogi, SP William Ovye Aya, ya ce yana jiran cikakken rahoto daga DPO na yankin kafin ya bayar da ƙarin bayani. Majiyar ta kuma buƙaci a ƙara yawan jami’an tsaro a yankin da sauranɓm ɓɓ wuraren da ake fargabar barazanar tsaro.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja

Ya ce ya sayi layin wayar ne daga hannun wani Audu, ɗan kungiyar Vikings wanda ya tsere yanzu.

A wani lamari kuma, ‘yansanda sun kama wasu mutum huɗu da suka shiga gonar wani mutum a Lapai Gwari, inda suka saci kifi da darajar kuɗinsu ta kai Naira 750,000.

Babban wanda ake zargi, Hussaini Garba, ya amsa laifi tare da bayyana Ahmed Yusuf, Ibrahim Musa da Abdulazeez Bawa a matsayin mutanen da suke sayen kifin idan ya sato.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • An Karrama Farfesa Adamu Gwarzo Kan Gudummawarsa Ga Bunƙasa Ilimin Jami’a A Nijeriya
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi