Gwamna Peter Mbah Ya Ƙaddamar Da Jiragen Kasuwanci 3 Na ‘Enugu Air’ Mallakin Jihar
Published: 7th, July 2025 GMT
Kamfanin jirgin sama mallakar jihar Enugu, wato Enugu Air, ya fara aiki a hukumance ranar Litinin bayan ƙaddamar da shi a filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu.
Mutane da dama sun halarci bikin ƙaddamarwar tare da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, da sauran manyan baki da suka halarci bikin ƙaddamarwar.
Enugu Air wani ɓangare ne na hangen nesa da ƙudurin Gwamna Peter Mbah, don inganta harkar sufuri da mayar da Enugu cibiyar jiragen sama a Nijeriya. Kamfanin ya fara aiki da jirage uku na Embraer E170 da E190, wadanda suka dace da zirga-zirgar cikin gida.
Jirgin zai fara tashi tsakanin Enugu da Abuja da kuma Jihar Legas, sannan ana shirin faɗaɗa jigilar zuwa sauran manyan birane kamar Port Harcourt da Owerri da Benin da kuma Jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Festus Keyamo
এছাড়াও পড়ুন:
Hadimin Gwamnan Yobe Ya Fice Daga APC Ya Koma Jam’iyyar ADC
Ɗaya daga cikin hadiman gwamnan jihar Yobe, Hon. Babagana Yakubu Mohammed, ya ajiye muƙaminsa na mai taimakawa gwamna na musamman ya kuma fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC.
Babagana, ya sanar da ajiye aikin nasa ne cikin wata wasiƙa da ya aikewa Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Malam Wali.
Ba Ni Da Niyyar Barin APC Zuwa Wata Jam’iyyar — Gwamna Zulum Ranar Talata Mai Zuwa Zan Koma Zauren Majalisar Dattawa – Sanata NatashaA kwafin wasiƙar da LEADERSHIP ta samu, Babagana ya bayyana matuƙar damuwarsa kan yadda aka yi watsi da wanda suke hidimtawa gwamnati da taimaka mata. “Don haka ina sanar da ajiye aiki na a hukumance daga matsayin mai taimakawa gwamna na musamman” cewarsa.
A ƙarshe, ya godewa gwamna Buni bisa damar da ya ba shi na yin aiki a gwamnatinsa, tare da yi masa fatan alheri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp