HausaTv:
2025-12-08@04:18:40 GMT

Sojojin Kasar Yemen Sun Kai Wa HKI Hari Da Makami Mai Linzami

Published: 19th, March 2025 GMT

A ci gaba da taya Falasdinawa fada da sojojin Yemen suke yi, sun kai wa sansanin jiragen sama na HKI dake saharar “Nakab” hari da makami mai linzami samfurin “Ballistic’ wanda ya fi sauti sauri.

A wata sanarwa da sojojin Yemen su ka yi da marecen jiya Talata sun bayyana cewa; a karkashin taimakawa Falasdinawa da ake zalunta, da kuma mayar da martani akan kisan kiyashin da abokan gaba ‘yan sahayoniya suke yi wa ‘yan’uwanmu a Gaza, sojojin Yemen sun kai hari da yardar Allah  akan sansanin sojan sama na Nivatim” da makami mai linzami wanda ya fi sauti sauri, mai suna “Falasdinu 2” sun bisa yardar Allah ya isa inda aka harba shi.

Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa; Sojojin Yemen za su fadada hare-haren da suke kai wa a cikin Falasdinu dake karkashin mamaya a cikin sa’o’i da kuma kwanaki masu zuwa, matukar abokan gaba ba su daina kai wa Gaza hare-hare ba.”

Kakakin sojan Yemen janar Yahya Sari ya kuma bayyana cewa; al’ummar Yemen da ta kunshi jagorori, al’umma da kuma soja, ba za su zama ‘yan kallo ba ana yi wa ‘yan’uwanmu kisan kiyashi a Gaza.” Har ila yau janar Sari ya ce; “ Bisa yardar Allah  sojojin na Yemen za su yi amfani da dukkanin makaman da take da su domin kare da taimakon Falasdinawa da ake zalunta.”

Janar Sari ya kuma ce; Ba za su daina kai hare-haren ba, har zuwa lokacin da za a dakatar da  killace Gaza da ci gaba da kai musu kayan agaji a suke da bukatuwa da su, kuma za su ci gaba da hana jiragen ruwa wucewa zuwa HKI.

A gefe daya, sojojin na Yemen sun sanar da sake kai hari akan jirgin dakon jiragen yaki na Amurka dake cikin tekun “Red Sea” wanda shi ne karo na 4 a cikin sa’o’i 72.

 Janar Sari ya kuma sanar da cewa sun yi nasarar dakile wani hari da ake gab da kai wa Yemen ta sama,kuma hare-haren na Amurka ba za su hana su ci gaba da hana su aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu ba na addini da ‘yan’adamta dangane da al’ummar Falasdinu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno

’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su, masu shekaru hudu da biyar, a Jihar Borno.

An ceto yaran ne a yayin wani samame da ’yan sanda suka kai a Ƙaramar Hukumar Jere, inda masu garkuwar suka je karbar kuɗin fansa.

Sanarwa da ASP Nahum Kenneth Daso, kakakin rundunar ya fitar ta ce, bayan sun sami rahoto a ranar 4 ga Disamba cewa yara uku sun bace, washegari masu garkuwar suka sako ɗaya daga cikin yaran da takardar neman naira miliyan 10 domin sakin sauran biyun.

A ranar ce jami’an rundunar suka kai samame a wurin da aka ware don karɓar kuɗin fansar.

Ganin hakan masu garkuwa da mutanen, suka farga da wannan tarko da aka musu nan da nan suka yi watsi da yaran suka gudu cikin duhu.

An ceto yaran ba tare da wani rauni ko biyan kuɗin fansa ba, kuma sun sake haɗuwa da iyalansu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano waɗanda ake zargi.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Yobe, Naziru Abdulmajid, ya ba da umarnin zurfafa bincike kuma ya umurci jami’an rundunar da su qarfafa sintiri, su gudanar da ayyukan bincike mai tsauri, da kuma ci gaba da gudanar da ayyukansu don rage yawaitar aikata laifuka a baya-bayan nan.

Hukumar tsaron ta kuma yi kira ga mazauna yankin da su kasance cikin shiri da kuma bayar da rahoton ayyukan da ake zargi, tare da samar da lambobin tuntuɓar gaggawa don hanzarta kai xauki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato
  • ’Yan bindiga ya hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166
  • Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba
  •  Dubban Mutane Suna Guduwa Daga  Gabashin DRC Saboda Barkewar Sabon Fada
  • Mutane Biyar Ne Suka Mutu A Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojojin Afghanistan Da Pakistan
  • ’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno
  • Sojojin Afganistan Da Pakistan Sun Yi Musayar Wuta A Tsakaninsu Duk Tare Da Tsagait Wuta
  • Nigeria: Har Yanzu Da Akwai Daliban Makaranta 250 Da Suke Hannun Masu Garkuwa Da Su
  • Limamin Tehran:  Idan Abokan Gaba Su Ka  Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa