Aminiya:
2025-07-07@19:12:24 GMT

Amurka za ta ɗauki nauyin ’yan tawaye domin yaƙi da ta’addanci

Published: 7th, July 2025 GMT

Ma’aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta ware dala miliyan 130 a kasafin kudinta na 2026 karkashin Yaƙi da ISIS da Kudin Kayan Aiki (CTEF) don taimaka wa kungiyoyi masu dauke da makamai a Syria, cikin su har da SDF da YPG ta mamaye.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da Siriya ke ci gaba da fuskantar rashin kwanciyar hankali da kalubale masu yawa tun bayan kawo karshen mulkin Bashar al-Assad.

Bidiyon tsiraici: Babiana ta sake jawo ce-ce-ku-ce Madatsar Ruwan Lagdo na yi wa jihohi 3 na Nijeriya barazanar ambaliya

Manyan matsaloli sun haɗa da kasancewar kungiyoyi masu dauke da makamai daban-daban, rikice-rikicen filaye da ba a warware ba, tsoma bakin sojojin ƙasashen waje, da tattalin arziki mai rauni wanda ke fama da talauci da kuma ƙaura ta yawan jama’a.

Gwamnatin rikon kwarya ƙarƙashin jagorancin Ahmed al-Sharaa na fuskantar ƙalubale wajen neman sahihanci da amincewa, tare da barazana daga mabiyan Assad, ragowar mayakan ISIS, da hare-haren ‘yan tawayen.

Akwai kuma damuwa kan rawar da HTS ke takawa — kungiyar da ta jagoranci kifar da mulkin Assad — da kuma yiwuwar ta zama mai mulkin danniya.

Sai dai asu takardu na Ma’aikatar Tsaron Amurka sun kare kasafin kudinta na 2026, inda suka ce kudaden na da manufar horarwa, bayar da kayan aiki, da albashin wata-wata ga SDF da Mayakan Sa Kai na Syria dubu 19 da Amurka ke goya wa baya a Kudu maso Gabashin Syria, tare da wasu abokan aiki a Iraƙi da Lebanon.

Bayanan sun nuna cewa kayayyakin sun haɗa da ƙananan makamai tare da kayan kula da lafiya a kayan gyara, “kuma dawowar ‘yan ta’addar Daesh na barazana ga tsaron Amurka, jama’ar Iraƙi, Syria, Lebanon da ma jama’ar duniya baki ɗaya.’

YPG reshen PKK ne a Syria, kungiyar da Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ta ta’adda, kuma kaso mafi tsoka da Pentagon ta ware a kasafin ya tafi ga ’yan tawayen PKK/YPG.

Daga cikin dala miliyan 130 da aka ware saboda Syria a kasafin kudin Pentagon na 2026, dala miliyan 7.42 za ta tafi ga Mayakan Sa Kai na Syria PKK/YPG, inda bayanan suka ce ana sa ran “kara karfinsu” wajen yaki da gyaran ‘yan ta’addar Daesh a Saharar Badiyah, sai dai kuma mafi yawan kudaden za su tafi ne ga ’yan tawayen SDF.

Kudaden baya-bayan nan na zuwa ne bayan an ba su dala miliyan 147.9 a 2025 da dala miliyan 156 a 2024, duk da sunan yaki da ‘yan ta’addar Daesh, matakin da Turkiyya ta nuna kin amincewa da shi saboda ana fakewa da hakan ana bai wa ‘yan ta’adda makamai a kan iyakarta.

A Ayyukan ta’addancin da ta ɗauki shekaru 40 tana yi, PKK, kungiyar da Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ta ta’adda, ta kashe fiye da mutum 40,000, ciki har da fararen hula, mata, da yara kanana.

Jaridar Kurdistan ta ruwaito Turkiyya nanata cewa bai wa ‘yan ta’addar PKK/YPG makamai ko ma da sunan mene ne, taimaka wa ta’addanci ne kai tsaye.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Turkiyya yan ta addar dala miliyan

এছাড়াও পড়ুন:

Gonakin Koko: Mata sun yi barazanar zanga-zanga tsirara a Kuros Riba

Wasu ƙungiyoyin mata a ƙauyukan Bendeghe-Ekiem da Abiya da ke Ƙaramar Hukumar Etung, a Jihar Kuros Riba, sun yi  barazanar gudanar da zanga-zangar tsirara idan gwamnati ba ta janye ƙudirin sayar da gonakin koko ba.

Matan sun ce wannan shawara da gwamnati ta ɗauka ba su aminta da ita ba, domin gonakin koko su ne tushen rayuwarsu, wanda da su suke cin abinci, suke biya wa ’ya’yansu kuɗin makaranta.

Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a Kano

Aminiya ta samu rahoton cewa gwamnati na shirin sayar da hannun jarinta a wasu manyan gonakin koko da ke wannan yanki, wanda hakan ya fusata matan da sauran al’ummar ƙauyukan da abin ya shafa.

Majiyarmu ta ce, “Idan gwamnati ta sayar da hannun jarinta, to tamkar hana mu cin moriyar aikin gonarmu ne. Wannan mataki ya saɓa wa yarjejeniyar da aka taɓa yi a baya.”

A ƙarshen mako, wasu daga cikin matan sun gudanar da zanga-zanga r lumana don nuna rashin amincewarsu da wannan ƙudiri.

Sai dai duk da ƙoƙarin sasanci daga Ma’aikatar Ayyukan Gona ta jihar, matan sun bai wa gwamnati wa’adin mako biyu ta janye shirin, ko kuma su fito su yi zanga-zangar tsirara.

Shugabannin ƙungiyoyin matan; Ntunkai Mary Obi da Cif Helen Ogar, sun roƙi Kwamishinan Ayyukan Gona, Johnson Ebokpo, da ya kai wa gwamnan kokensu, domin a samu mafita kan lamarin.

“Mun bai wa gwamnati mako biyu ta janye wannan ƙudiri ko kuma a zauna da shugabanninmu domin a cimma matsaya.”

Baya ga matan, wasu shugabannin matasa da dattawan yankin irin su Kwamared Tandu Kingsley da Mista Etta Atu-Ojua, sun goya matan baya.

Sun ce: “Idan gwamnati ta sayar da gonakin, matasa ba za su ƙara samun abin yi ba, kuma hakan zai jefa wasu cikin ayyukan daba da sata.”

Sun buƙaci gwamnatin ta sake nazari da idon basira, domin kada al’umma su shiga cikin ƙalubalen rayuwa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kaddamar Da Shirin Samar Da Wutar Lantarki A Jami’ar Kashere Gombe.
  • Malamin Addinin Musulunci Yayi Kira Da Ayi Gaggawa Gyaran Hanyar Zamfara
  • AI Zai Maye Gurbin Ayyuka Miliyan 92 A Duniya – Farfesa Pate
  • Sanata Dickson Ya Buƙaci ‘Yan Nijeriya Da Su Yi Yaƙi Da Matsalar Sayen Ƙuri’a
  • Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC
  • Gonakin Koko: Mata sun yi barazanar zanga-zanga tsirara a Kuros Riba
  • Jaridar Telegraph: Makaman Iran Masu Linzami Sun Sauka Kai Tsaye Akan  Cibiyoyin Sojan Isra’ila Guda 5  
  • Dalilin Kwararru Na Bukatar Kafa Cibiyoyin Bincike Kan Nau’ikan Dabbobi A Nijeriya
  • Shirin Tinubu Kan Kiwon Dabbobi Zai Samar Da Ayyukan Yi Miliyan 5 Ga Matasa – Jega