Firaministan Kasar Sin: Kasarsa Ta Kimtsa Tsaf Wajen Inganta Aikin BRI Da Bunkasa Kasuwanci Da Zuba Jari Tare Da Habasha
Published: 7th, July 2025 GMT
A nasa bangaren, Abiy ya ce Habasha da Sin amintattun kawaye ne na manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, kuma kasarsa tana mika tsantsar godiya ga kasar Sin saboda goyon bayan da ta dade tana bai wa Habasha a fannin raya tattalin arziki da zamantakewa.
Yayin da yake nuni da irin muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a harkokin kasa da kasa, musamman a fannin raya ci gaban duniya, Abiy ya ce Habasha a shirye take ta rubanya mu’amala a matakin koli da kasar Sin da kuma zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Maduro Ya Jinjina Wa Jagororin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro wanda ya bude bikin baje kolin littatafai na kasa da kasa a kasarsa, ya yi jinjina ga Imam Khumaini ( r.a) da kuma jagoran juyi Ayatullah Sayyid Ali Khamnei.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto cewa, A yayin bikin bude taron baje kolin, shugaban kasar na Venezuela ya bayyana girmamawar da yake yi wa jagoran juyin musulunci, tare da yin ishara da ganawarsu a shekarun 2000 da 2010.
Haka nan kuma shugaban kasar ta venezuella ya bayyana yadda ya ga al’adu da ci gaban al’ummar Iran da su ka ja hankalinsa da burge shi matuka.
Bugu da kari shugaba Maduro ya bayyana zurfin hikimar da ya gani a tare da jagoran juyin musulunci, da kuma yadda yake kare tsarin jamhuriyar musulunci da ci gaba da wanzuwarsa a cikin nutsuwa, hakuri, juriya da kuma tsayin daka.
Har ila yau, shugaba Maduro ya yi ishara da yadda Iran take cika alkawalinta a fagen kawancenta da kasarsa Venezuela.