Kano ta sami rahoton cin zarafin yara 351 – NHRC
Published: 7th, July 2025 GMT
Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC) a jihar Kano ta ce ta samu rahoton laifuka 351 na take hakkin yara daga cikin jimillar kararraki 446 da ta samu daga watan Afrilu zuwa Yuni 2025.
Kodinetan NHRC na jihar Kano Alhaji Shehu Abdullahi ne ya bayyana haka a Kano.
Ya bayyana cewa daga cikin jimillar korafe-korafe 446 da aka samu a cikin watanni uku 351 na da alaka da take hakkin yara.
Ko’odinetan jihar ya yi nuni da cewa, sauran shari’o’in sun hada da tashin hankalin gida 19, 18 da suka shafi ‘yancin tattalin arziki da zamantakewa, da kuma biyar da suka shafi ‘yancin rayuwa.
“cikin zarge zargen har na Maita da sauran shari’o’in da suka shafi take hakkin dan adam”
A cewar Alhaji Shehu, yanayin zamantakewar al’umma a halin yanzu yana nuni da yadda ake tauye hakkin yara, wanda hakan ya nuna yadda ake kara yawaitar yaran da ke yin bara a tituna da kuma rayuwa cikin mawuyacin hali.
“Sakaci na iyali da al’umma shi ne babban abin da ke haifar da cin zarafin yara da kuma karuwar ayyukan aikata laifuka a tsakanin matasa.”
Ko’odinetan hukumar ta NHRC ya jaddada cewa, yayin da bakwai kawai daga cikin wadanda aka bayar da rahoton an aikata su ne ta hannun masu fada aji kuma yana farywa a cikin gidajen aure.
“Iyali su ne tushen al’umma, al’umma kuma ita ce al’umma, saboda haka, duk wani cin zarafi a cikin iyali zai yi naso a kan al’umma baki daya.”
Ya kara da cewa “Lokacin da aka samu babban cin zarafi a cikin iyali, ba za a iya samun ci gaba mai ma’ana a cikin al’umma mafi girma ba.”
Alhaji Shehu ya ci gaba da cewa, daga cikin korafe-korafen da aka samu, an gudanar da cikakken bincike da kuma kammala shari’o’i 341, yayin da 105 ke ci gaba da sauraron karar.
Ya yi kira ga jama’a da su samar da zaman lafiya da juna tare da kai rahoton duk wani da ake zargi da take hakkin dan Adam ga hukumomin da abin ya shafa.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, NHRC tana aiki ne a matsayin wata hanya mai zaman kanta don tabbatar da mutuntawa, kariya, da kuma inganta hakin bil’adama a Najeriya.
Khadija Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kare Hakki
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan
Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya ce afuwar shugaban ƙasa ya yi masa, ta ba shi kwarin guiwar yin wata sabuwar tafiyar siyasa.
Ya bayyana cewa ya bar tafiyar Kwankwasiyya ne saboda jagorancinta ya yi watsi da shi lokacin da ya fi bukatrsu.
’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace dabbobi a Katsina Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEFLawan, wanda ya wakilci mazabar Bagwai/Shanono a Jihar Kano, yana cikin mutane 175 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa afuwa a ranar 9 ga watan Oktoba.
An kama shi a shekarar 2021 bayan samun sa da laifin karɓar cin hanci a 2012, domin cire sunan wani kamfani daga jerin waɗanda ake zargin suna da hannu wajen tafka almundahana a tallafin man fetur.
Bayan ya kammala zaman gidan yari, an sake shi a watan Oktoban 2024.
Lawan, ya ce wannan ta sauya masa tunani game da siyasa da aminci.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Lawan, ya bayyana cewa tafiyar Kwankwasiyya ta yi watsi da shi, duk da cewa ya dade yana cikin tafiyar.
“Idan Allah Ya jarabce ka, zai nuna maka waye na gaskiya a cikin abokanka,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa wani muhimmin jagora a tafiyar bai taɓa kira ko yi masa jaje ba lokacin da yake gidan yari ko bayan fitarsa.
“Yanzu shekara ɗaya kenan da fitowa ta, amma bai kira ni ba ko ya ce ‘Allah ya taimake ka ba’,” in ji Lawan.
Lawan ya bayyana cewa a lokacin da yake a gidan yari, ya umarci magoya bayansa su shiga jam’iyyar NNPP a lokacin zaɓen 2023.
Amma yanzu yana ganin jam’iyyar karama ce da burinsa na siyasa.
“Siyasa ya kamata ta zama mai faɗi, amma yanzu NNPP ta yi mini ƙarama,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa yanzu zai mayar da hankali kan siyasar ƙasa baki ɗaya, maimakon yin tafiya a waje guda.