Jami’an Leken Asirin “Shabak” Na Isra’ila Sun Kama Nasir Lahham Na Tashar Talabijin din Almayadin
Published: 7th, July 2025 GMT
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; kungiyar leken asirin HKI ta cikin gida, “Shabak” ta kama shugaban ofishinta a Falasdinu dake karkashin mamaya Nasir al-Lahham, a gidansa da yake a garin Beithlaham.
Majiyar ta kara da cewa; Jami’an kungiyar leken asirin ta “Shabakh” sun dade suna binciken dakin watsa labarin da Lahham yake watsa shirye-shiryensa.
Tashar ta “Almayadin’ dai ta bayyana cewa kamun da aka yi wa ma’aikacin nata yana a karkashin Takura mata ne da HKI take yi, domin a cikin watan Oktoba na 2023 ma dai jami’an tsaron sun kai hari cikin gidansa, su ka ci zarafin maidakinsa da kuma kama ‘ya’yansa Basil da Baasil.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam ” Nahid 2″ Da Zai Samar Wa Yankunan Karkara Hanyar Sadarwa Ta “Internet”
Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta.
Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin gwajin da hakan yake a matsayin wani ci gaba a fagen sadarwa a Iran.
Har ila yau ministan Sadarwar Sitar Hashimi ya kuma ce; A tsakanin kauyuka 10,000 da ba su da hanyoyin sadarwa, yanzu an rage su da 2000, kuma ana ci gaba da aiki tukuru domin isa ga kauyunan da suke nesa,masu wahalar zuwa.
Ministan sadarwar na Iran ya kuma kara da cewa; ma’aikatarsa tana son amfani da tauraron dan’adam domin fadada hanyoyin sadarwa na internet wanda yake da inganci sosai, kuma zai samarwa da dukkanin yankunan karkara hanyoyin sadarwa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea September 17, 2025 Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro September 17, 2025 Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar Kasuwanci Da HKI September 17, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa Kisan Kiyashi A Gaza September 17, 2025 Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila September 17, 2025 Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta September 17, 2025 Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha September 17, 2025 Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa September 17, 2025 Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci