Maniyatan Jihar Kaduna Na Bana Sun Fara Karbar Horo
Published: 29th, January 2025 GMT
Hukumar Alhazan Jihar Kaduna ta Kaddamar da shirin bada horo da fadakarwa ga maniyatan bana
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa an gabatar da wannan bitar ko horon ne a cibiyar hukumar alhazai ta jihar Kaduna da ke unguwar Dogarawa a karamar Hukumar Sabon Garin Zaria.
Shugaban hukumar na jihar Kaduna Malam Salihu Abubakar yace bitar wani jigo ne ga kokarin da ake wajen ilmantar da maniyata yadda zasu sauke farali salun alun.
Za a fadakar da maniyatan game dukkanin abubuwan da suka shafi aikin hajji domin fuskantar kowane irin kalubalen da zai taso lokacin aikin hajji mai zuwa.
Malam Abubakar ya roki mabiyatan su kammala biyan kudin aikin bana kafin cikar wa’adin da hukumar aikin hajji ta kasa ya cika wacce ta warewa jihar Kaduna maniyata dubu 6.
A jawabinsa, shugaban sashen gudanarwa na hukumar aikin hajji ta jihar Kaduna Alhaji Abubakar Usman Yusuf yayi bayanin cewa za a ci gaba da bada wannan horon a kowane karshen mako a dukkanin kananan hukumomin jahar 23.
Shi kuma.shuganan karamar hukumar Sabon Garin Zaria Malam Jamilu Abubakar Albani wanda ya samu wakilcin mataimakin sa Alhaji Abdulkareem Kamalu ya jaddada bukatar maniyata su kiyaye dokokin kasar Saudiyya dama na Nijeriya a lokacin aikin hajjin bana.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: jihar Kaduna
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar
Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp