Majalisar Dattawa Ta Dakatar Da Sanata Natasha Na tsawon Watanni 6 Saboda Rashin Da’a
Published: 6th, March 2025 GMT
Don haka, Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida saboda saba ka’idojinta na majalisar dattawa.
Bugu da kari, majalisar ta bukaci Natasha da ta maido da duk wani abu mallakin majalisar ga mai kula da Majalisar har sai lokacin dakatarwar ya cika.
Sanata Imasuen ya bayyana cewa, “A madadin kwamitin majalisar dattawa kan da’a, gata, da kuma sauraron kararrakin jama’a, muna godiya ga shugaban kasa da manyan abokan aikinmu bisa damar da aka ba mu na yi wa ‘yan Nijeriya hidima ta hanyar wannan kwamiti.
Bayan doguwar muhawara kan rahoton da kwamitin ya gabatar, Sanatocin sun amince da dukkan shawarwarin ta hanyar kada kuri’a tare da yin kwaskwarima ga shawara ta 6, inda aka bai wa mataimakan Sanata Natasha damar karbar albashi da alawus-alawus din su domin kada su tagayyara.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, dukkan Sanatocin da suka yi magana sun nuna goyon bayansu ga sakamakon binciken.
A yayin da Sanatocin suka amince da shawarwarin, Sanata Natasha ta yi tsinkaye kan zaman, inda ta ce zalincin da aka yi mata ba zai dore ba. Daga nan aka fito da ita daga dakin zauren majalisar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Takht Ravanji: Iran Ba Za Ta Taba Yin Tattaunawa Akan Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium Ba
Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a Iran ba, ko kuma batun makamanta masu linzami.
Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa, wadannan abubuwan biyu wato dakatar da ci gaba da tace sanadarin uranium da kuma makamai masu linzami, jan layi ne da jamhuriyar musulunci ta Iran ba za ta bari a ketara su ba ba kuma za ta bari a bude tattaunawa akansu ba.
Kwamitin da yake kula da tsaron kasa da kuma siyasar waje a majalisar shawarar musulunci ta Iran a karkashin jagorancin dan majalisar Ibrahim Ridhazi ya yi taro a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka gayyaci mataimakin ministan harkokin wajen domin jin ta bakinsa akan abubuwan da suke faruwa a tattaunawar da ake yi ba kai tsaye ba da Amurka.
Ridha’i ya fada wa ‘yan jarida cewa Takht Ravanji ya kammadar da rahoto akan yadda tattaunawar take gudana a tsakanin Amurka da Iran da kasar Oman take shiga Tsakani.
Haka nan kuma ya ce; Tace sanadarin Uranium a cikin gida wani jan layi ne da ba za a tsallake shi ba.