Tsaro: Gwamna Lawal Ya Jaddada Aniyar Gwamnatinsa Na Bai Wa Sojoji Haɗin Kai
Published: 7th, March 2025 GMT
“Ina son in nuna jin daɗina ga Babban Hafsan Sojin Sama, wanda kafin ziyarar tasa a yau, ya aiko da wata tawaga mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin manyan hafsoshi daga hedikwatar domin jajanta mana da al’ummar Zamfara. Ya aika da tawaga zuwa Zamfara a lokuta biyu daban-daban.
“Ina son nanata cewa a lokacin da lamarin ya faru, mun yi magana da manema labarai, inda muka fayyace cewa ba da gangan ba ne, illa hatsari ne.
Gwamnan ya bayyana cewa rundunar sojin saman Nijeriya na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙar ‘yan bindiga a Zamfara, Arewa maso Yamma, da ma kasa baki ɗaya. “Ina godiya da babban hafsan sojin sama bisa gudunmawar da rundunar ta bayar. Suna amsa kiran gaggawa a duk lokacin da muka buƙata.
“Mun fito ƙarara game da matsayinmu. Mun sanar da duk mai saurare cewa ba mu shirya ba kuma ba za mu taba yin sulhu da ‘yan bindiga ba. Kowa na iya tabbatar da cewa matsayinmu yana samun sakamako, domin mun fara ganin sakamako mai kyau, sannu a hankali zaman lafiya ya dawo Zamfara.
“Ina so in yi amfani da wannan damar in sanar da Air Marshal cewa muna gina filin jirgin sama a Zamfara. Ina roƙon cewa da zarar an kammala filin jirgin, muna son hangar sojojin sama don tabbatar da kowa ya tafi daidai a jihar.
“Za mu ci gaba da tuntubar ku saboda muna buƙatar sojojin sama. Ba za mu iya gode maka a a kan wannan ziyarar ba. A gare mu a Zamfara, mun jinjina wa wannan tattaki da ku ka yi tun daga Abuja. Daga bangarenmu, ina tabbatar muku cewa za mu ci gaba da yin cudanya da ku, kuma za mu yi duk mai yiwuwa don tallafa wa sojojin da ke yaƙi da ’yan bindiga. Ina yi muku fatan sauka lafiya a Abuja.”
A farko, Babban Hafsan Sojin sama Air Marshal Hassan Bala Abubakar, ya miƙa godiyarsa ga gwamna Dauda Lawal bisa haɗin kan da ya bayar wajen faɗakar da al’umma kan harin da aka kai bisa kuskure a Zamfara.
“Idan za ku iya tunawa a ranar 11 ga watan Junairu, 2025, an kai hare-hare ta sama a Zamfara sakamakon rahoton sirri na ‘yan bindiga a Gidan Makera a ƙaramar hukumar Maradun. An kai harin ne da nufin fatattakar ‘yan ta’addan da ke da alaƙa da ɗan fashin daji Bello Turji. Kwanaki kaɗan bayan harin, wani rahoto ya yi ikirarin cewa jirgin ya kai harin ne kan wasu ‘yan ƙungiyar ‘yan sintiri bisa kuskure.
“Saboda damuwa da wannan zargi, nan da nan na kafa kwamitin bincike kan harin. Tuni dai kwamitin binciken ya gabatar da rahotonsa da sakamakon binciken, wanda ya tabbatar da cewa an kashe ‘yan sintiri 11 ba da gangan ba.
“Ziyarar mu ta safiyar yau mun yi ta ne don jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa, da kuma al’ummar Zamfara bisa wannan mummunan lamari.”
Gwamnan da hafsan sojin sama sun yi wata ganawar sirri da iyalan waɗanda harin jirgin ya rutsa da su, tare da wasu 11 da suka jikkata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Dr Najib Hussaini Adamu, a matsayin Amirul Hajj na Jihar Jigawa, kuma shugaban tawagar Gwamnatin jihar domin gudanar da aikin Hajjin 2025.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai.
Gwamnan ya kuma amince da nadin mambobin tawagar Amirul Hajjin.
Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa, mambobin sun hada da Dr. Yusuf Abdurrahman, Babban Limamin Masarautar Hadejia da Alhaji Lawan Ya’u Roni, Talban Kazaure.
Sauran su ne Dr. Mahmoud Yunusa, Sa’in Dutse da kuma Alhaji Adamu Dauda Zakar, Durbin Hadejia.
Sanarwar ta bayyana cewa an yi wadannan nade-nade ne bisa la’akari da irin kwazon da suka nuna a ayyukansu, sadaukarwa, kishin kasa, amana da kuma tsoron Allah.
A cikin sakon taya murna ga wadanda aka nada, Sakataren Gwamnati ya bukace su da su ci gaba da nuna wadannan dabi’u yayin da za su gudanar da wannan muhimmin aiki da aka dora musu, don kara tabbatar da amanar da gwamnatin da al’ummar Jihar Jigawa suka dora a kansu.
Sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran tawagar Amirul Hajjin za ta yi aiki kafada da kafada da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa da kuma sauran hukumomin da suka dace a matakin Jiha, Tarayya da na kasa da kasa domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da inganci.
Sanarwar ta bayyana cewa nade-naden sun fara aiki nan take.
Usman Muhammad Zaria