Sin Na Maraba Da Jarin Kasa Da Kasa A Fannin Kamfanonin Fasaha
Published: 6th, March 2025 GMT
Gwamnan babban bankin kasar Sin Pan Gongsheng, ya ce Sin na maraba da masu zuba jari na sassan kasa da kasa, da su shigar da jarinsu cikin kamfanonin fasaha na Sin.
Pan Gongsheng, ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a Alhamis din nan, a gefen zaman majalissar wakilan jama’ar kasar Sin na 14 dake gudana, yana mai cewa, a daya hannun kasar Sin na adawa da matakan siyasantarwa, da yin matsin lamba a harkokin da suka shafi zuba jari a kasuwanni, da ma kafa wasu shingaye na rashin adalci a fannonin zuba jari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA