Gwamna Nasir Ya Ƙaddamar da Aikin Titin Koko–Zuru Kan Naira Biliyan 64
Published: 29th, January 2025 GMT
Ya gargaɗi kamfanonin da suka samu kwangilar da su tabbatar da ingantaccen aiki, tare da jaddada cewa za a hukunta duk wanda ya kasa cika sharuɗan aikin.
Sannan, ya buƙaci direbobin manyan motoci da su guji lodin da ya fi ƙarfin titin domin kare lafiyar matafiya da rage hatsari.
Don haka, gwamnati za ta kafa kwamiti don tabbatar da bin doka da oda a kan titin.
Kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Abdullahi Umar Faruk, ya bayyana cewa kashi 40 na kuɗin aikin an riga an biya.
Ya ce an biya kamfanonin kuɗin kamar haka:
Kamfanin ZBBC zai shimfiɗa titin daga Dabai zuwa Mahuta (kilomita 25) a kan Naira biliyan 18. Kamfanin Habib Engineering LTD zai yi aikin daga Mahuta zuwa Marafa (kilomita 25) a kan Naira biliyan 18. Kamfanin GNIC zai yi aikin daga Koko zuwa Marafa (kilomita 37) a kan Naira biliyan 27.Baya ga titin Koko – Zuru, Gwamna Idris ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar za ta inganta babban asibitin Zuru domin ya zama cibiyar ƙwararru.
Haka nan, a yayin ziyarar godiya da ya kai ƙananan hukumomin Fakai, Sakaba, Danko Wasagu, da Zuru, ya kuma ƙaddamar da wata hanyar karkara mai tsawon kilomita 11 daga Koko zuwa garin Kangin Korama, wanda aikin zai ci Naira biliyan 1.3.
কীওয়ার্ড: Gwamna Nasir kan Naira biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu.
Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina makarantu kawai ba, yana ta’allaka ne ga ingancin malamai, kayan koyarwa da kuma yanayin makarantu.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara ɗaukar malamai tare da horas da su akai-akai domin rage cunkoson ɗalibai da malamai da kuma horar da su sabbin dabarun koyarwa.
“Wannan shiri ɗaya ne daga cikin mafi kyawu da muka gani. Idan wani ya yi kuskure, sai a hukunta shi, yayin da duk wanda ya yi fice, wajibi ne a yaba masa. Wannan shi ne yadda ake samun cigaba,” in ji gwamnan.
Ya bukaci sauran hukumomin ilimi kamar Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare, Hukumar Ilimin Addinin Musulunci, da Ma’aikatar Ilimin Firamare su yi koyi da wannan tsari domin ƙara ƙarfafa gwanintar malamai a dukkan matakai.
Gwamnan ya kuma sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da maida hankali wajen gina makarantu, horar da malamai, da walwalar su.
Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da baiwa bangaren ilimi goyon baya don inganta sakamakon koyo a makarantu a fadin Jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria