An gudanar da taron kafa kungiyar masana masu binciken sararin samaniya mai zurfi ta kasa da kasa wato IDSEA a birnin Hefei dake lardin Anhui, yau Litinin. Wannan ita ce kungiyar masana kimiyya da fasaha ta kasa da kasa ta farko da kasar Sin ta kafa a fannin binciken sararin samaniya mai zurfi.

A cikin watan Afrilun bana ne majalisar gudanarwar kasar Sin ta amince da kafa kungiyar IDSEA, wadda kungiyoyi guda 5 suka ba da shawarar kafa ta tare, ciki har da cibiyar binciken duniyar wata da ayyukan binciken sararin samaniya ta hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin, da cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar Faransa mai suna “Planetary Exploration, Horizon 2061.

” Kuma ta zama wata kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa a fannin kimiyya da fasaha da ta yi rijista da hukumar da batun ya shafa.

Wu Weiren, babban mai tsara aikin binciken duniyar wata na kasar Sin, ya bayyana cewa, kafa wannan kungiyar na da matukar muhimmanci kan mu’amala da hadin gwiwar sararin samaniya tsakanin Sin da kasa da kasa. Ana gayyatar masana kimiyya da injiniyoyi daga fagen binciken sararin samaniya da kimiyya da fasaha na duniya don shiga cikin kungiyar, da ba da kyakkyawar gudummawa ga binciken sirrin sararin samaniya.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: binciken sararin samaniya

এছাড়াও পড়ুন:

Masanin Kenya: Kasashe Masu Tasowa Suna Bukatar Kasar Sin

Masanin Kenya kan huldar kasa da kasa mai suna Cavince Adhere, ya bayyana a yayin zantawarsa da dan jarida na kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan cewa, a matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa ya jaddada daidaito da samun albarkatu, inda hakan ya samu aminci daga kasashe masu tasowa. Kuma har ila yau, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashe masu tasowa ya riga ya samu gagarumin ci gaba, don haka makomar kasashe masu tasowa na bukatar ci gaba da kasancewar Sin a cikinsu.

Bugu da kari, Cavince Adhere ya jaddada cewa, Sin ta bayyana bukatun kasashe masu tasowa na duniya yadda ya kamata, kana tana inganta ra’ayoyin da suka dace da muradunsu, kamar yadda aka samu ci gaba da kuma bunkasa a tsarin BRICS. Cavince Adhere ya ce, “Ta hanyar kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, da zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa, da yin mu’amala da juna a fannin al’adu, da bullo da sabbin ra’ayoyi a fannonin raya kasa da kasa, Sin ta zama wani muhimmin karfi wajen gina tsarin dunkulewar kasa da kasa.”

Kazalika, ya ce, “Ko shakka babu, kasashe masu tasowa ma za su kasance wani karfi wajen inganta ci gaba mai dorewa a karni na 21.”(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Reuters: Amurka Tana Da Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza
  • Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Harin HKI A Kasar Yemen
  • Gwamnatin Kasar Iran Ta Yaba Da Kungiyar BRICS Saboda Yin Tir Da HKI A Yakin Kwanaki 12
  • Elon Musk zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka
  • Masanin Kenya: Kasashe Masu Tasowa Suna Bukatar Kasar Sin
  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce Kungiyar ECO Ta Yi Tir Da Hare-Haren HKI Kan Kasarsa
  • Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa
  • Dalilin Kwararru Na Bukatar Kafa Cibiyoyin Bincike Kan Nau’ikan Dabbobi A Nijeriya
  • Sheikh Na’im Kasim Yace Kare Kasa Baya Bukatar Izini Daga Wani