Asibiti Mai Zaman Kansa A Kano Zai Fara Aikin Manyan Tiyatu Tare Da Rage Kuɗi Kaso 50%
Published: 7th, July 2025 GMT
(ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne
(Dental) Hakori
(Fibroid) Qarin mahaifa,
(Urology) Aikin Mafitsara
Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya.
Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini BaHakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar Alfijir Labarai a safiyar Litinin.
Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga kuma yawan da mutane suka yiwa gwamnati shi yasa hukumar gudanarwar Asibitin Kwararru na Best Choice itama taga da cewar bada tata gudummawar domin kara karfafar gwamnati a wannan fannin.
Auwal ya kuma bayyana jin dadinsa ganin yadda al’umma suke ta cin gajiyar bude fiyil kyauta da rage kaso 50% ganin likita tare da manya da kananan ayyukan asibitin da yayi a satin da ya gabata.
Dukkannin waɗannan ayyuka za a fara gudanar da sune a yau Litinin, don haka ga masu irin wadannan matsaloli za su iya zuwa domin a tantancesu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Tiyata
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan
Wasu jerin shirye-shiryen neman ‘yancin kan Taiwan da hukumomin yankin suka gudanar a baya bayan nan, sun sha suka sosai daga al’ummomin kasa da kasa. Wani nazari da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa adadin mai rinjaye na wadanda suka shiga nazarin, watau kimanin kaso 89.8 sun yi ammana cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama wata matsaya da kasashen duniya suka amince da ita, inda suka soki hukumomin yankin Taiwan bisa shirinsu na neman ‘yanci da takala.
Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne cikin harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 13,650 suka bayar da amsa cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA