Amurka ce Kadai Ta Ki Yin Allawadai Da Killace Gaza A Tsakanin Mambobin Kwamitin Tsaro na MDD
Published: 19th, March 2025 GMT
MAfi yawancin mambobin kwamitin tsaron sun yi tir da harin da sojojin HKI su ka kai wa mutanen Gaza a cikin daren shekaran jiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar fiye da Falasdinawa 400.
Wakilin kasar Rasha a MDD ya bayyana cewa; Sake bude yaki a Gaza, yana nufin korar Falasdinawa daga kasarsu” ya kuma jaddada cewa; “ Wajibi ne ga kwamitin tsaro ya yi duk abinda zai iya yi, domin sake tsayar da wutar yaki, bai kuma kamata a ce an sake maimaita kurakuren baya ba.
Shi kuwa wakilin kasar Aljeriya a MDD, ya bayyana ya zargi HKI da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki, yana mai jaddada cewa; Wannan lokaci ne da hukunta masu laifi, domin babu wanda ya fi karfin doka.” Haka nan kuma ya ce; Yanzu duniya ta daina kawar da kanta daga laifukan da ‘yan mamaya suke yi.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi saboda matsalar tsaro
Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun firamare, sakandare, da manyan makarantu—ciki har da Gwamnatin Tarayya da makarantu masu zaman kansu saboda matsalolin rashin tsaro da ke faruwa a faɗin ƙasar kan.
Sanarwa da Jalaludeen Usman Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi, ya fitar ta ce, “Wannan shawara, duk da cewa tana da wahala, Gwamnatin Jihar Bauchi ta yanke ta ne bayan tattaunawa mai zurfi da kuma la’akari da matsalolin tsaro da suka shafi tsaron ɗalibai, malamai, da al’ummomin makarantu a faɗin jihar.”
“Gwamnati ta san abin da wannan matsala ka iya haifarwa. Duk da haka, kare ’ya’yanmu ya kasance babban nauyin da ke kanmu. Muna sane da cewa lowane ɗalibi a Jihar Bauchi ya cancanci ya yi karatu a cikin yanayi mai aminci, kwanciyar hankali, kuma ba tare da tsoro ba.
“Saboda haka muna kira ga iyaye, masu kula, masu mallakar makarantu, da duk masu ruwa da tsaki da abin ya shafa da kada su firgita, amma su kwantar da hankalinsu su kuma ba da haɗin kai.”
“Gwamnati tana aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro don magance matsalolin cikin sauri da kuma cikakkiyar fahimta, tare da tabbatar da cewa ayyukan ilimi na yau da kullum, za su ci gaba da gudana da zarar an tabbatar da hakan.
“Muna kuma kira ga jama’a da su ci gaba da taka tsantsan. Idan kun ga wani abu da ba ku gane ba ku bayar da bayani wa jami’an tsaro saboda bayar da bayanai da a kan lokaci suna da mahimmanci wajen kare al’ummominmu.
“Gwamnatin Jihar Bauchi za ta ci gaba da samar da sabbin bayanai yayin da lamarin ke ci gaba.”