Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira
Published: 19th, March 2025 GMT
Matatar Dangote ta sanar da dakatar da sayar da Man Fetur da Naira na wucin gadi.
Kamfanin ya bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ya aike wa dillalan man fetur a ranar Laraba da rana.
Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a RibasA cewar sanarwar, matatar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin guje wa matsalar biyan kuɗin ɗanyen mai da ta ke saya da dalar Amurka.
“Ya zuwa yanzu, mun sayar da sama da adadin man fetur da muka samu a Naira.
“Domin daidaita cinikayyarmu da sayen ɗanyen mai, dole ne mu ɗauki wannan mataki na wucin gadi,” in ji sanarwar.
Kamfanin Dangote ya kuma ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya dakatar da sayar.
Kamfanin ya ce wannan labari ba gaskiya ba ne, inda ya jaddada cewa tsarinsa yana da inganci kuma ba a samu wata matsala ba.
Matatar ta Dangote ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sayar da mai a Naira da zarar ta samu ɗanyen mai da aka sayar mata a Naira daga kamfanin NNPC.
“Muna nan daram wajen yi wa kasuwar Najeriya hidima, kuma za mu dawo da sayar da mai a Naira da zarar mun samu kaya,” in ji sanarwar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dalar Amurka da sayar da
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Daga Sani Sulaiman
Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu.
Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta.
Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan batun zaman lafiya tsakanin addinai.
Haka kuma, Dr. Kefas ya yabawa halayen Sheikh Bauchi, wanda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tawali’u, jin kai, da haƙuri.
Saboda haka, Gwamna Agbu Kefas ya yi kira ga jama’a da su yi koyi da jagorancin wannan fitaccen malami.
Ya ce al’ummar kasa za su ci gaba da bin tsarin ladabi da tarbiyyar da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya koyar.
A wani bangaren, Dr. Kefas ya ja hankalin ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da addininsu ba.
Ya jaddada muhimmancin jurewa da girmama ra’ayin juna maimakon nacewa a kan namu ra’ayin, tare da tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da hidima ga dukkan ‘yan Jihar Taraba bisa adalci ba tare da la’akari da addini ko kabilarsu ba.