Aminiya:
2025-12-12@21:06:23 GMT

Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah

Published: 19th, March 2025 GMT

Ga shi dai kwanakin Ramadan suna ta gudu, har mun kawo ga goman ƙarshe wanda shi ne dama ta ƙarshe ga wanda ya yi sakaci a farkon watan, ko kuma ya zama cikon alheri ga wanda ya kyautata ya bayar da abin da ake so a baya.

Ya ku masoya! Goman ƙarshe na watan Ramadan kasuwa ce babba da masu tsere suke tserereniya a cikinta.

Abubuwan da ba a sakaci da su a Ramadan —Sheikh Daurawa DAGA LARABA: Abin Da Ake Yi A Goman Tsakiyar Ramadan A Addini Da Al’ada

Lokaci ne da wanda ya yi sakaci yake ƙara ƙwazo a cikinsa, ake jarraba masu himma a cikinsa, ake tantance ma’abota Lahira da ma’abota duniya.

Da yawa masu huɗuba sun yi magana, masu wa’azi sun yi wa’azi, masu nasiha sun yawaita nasiha kan falalolin wadannan kwanaki da darare, zukatan da suka jiku da imani sun amshi wannan kira, wata jama’a ta amshi kiran ta bi hanyar muminai, ta koma cikin masu ruku’u da sujada, hawayensu na kwarara a tsakiyar dare mai duhu, kuma Ubangijinka Yana ji kuma Yana amsa musu, Ubangijinka bai zama Mai zaluntar bayi ba.

Wata jama’ar kuma ta ji kiran amma kamar ba ta damu ba. Suna jin muminai suna salloli da tsayuwar dare don ibada ga Ubangijinsu, amma su kamar ba su da bukata, kai kamar an yi musu lamunin Aljanna, shin masu wannan watsewa ba za su yi tunani ba?

Shin masu wannan sakaci ba za su sake tunani ba?

Ya ku Musulmi! Ranakun watanku suna raguwa, dararensa masu daraja suna karewa, suna masu shaida a kan abin da kuka aikata, suna kiyaye abin da kuka yi, su masu taskace kyawawan ayyukanku, masu tsarewa da adana su har zuwa lokacin da za a kira ku a Ranar Kiyama: “A Ranar da kowane rai ke samun (sakamakon) abin da ya yi.”

Ubangijinku Yana kira: “Ya ku bayiNa! Abin sani ayyukanku ne Nake kidaya muku kuma zan saka muku a kai.

Duk wanda ya samu alheri sai ya gode wa Allah, wanda ya samu wanin wannan kuma, kada ya zargi kowa sai kansa!”

Wannan watanku ne kuma wannan ne dama ta karshe, mutum nawa ne ya fara azumin bai kawo yanzu ba, ko ba zai kammala shi ba?

Kuma mutum nawa ya yi kwadayin dawowarsa a bana amma bai riske shi ba? Shin ba za ku yi nazari a kan ajali da makomarku ba?

Shin ba za ku dubi yaudarar da dogon buri yake yi muku ba?

Ya ku Musulmi! Idan akwai mai gargadi ga rayuka ko mai wa’azi ga zukata, to, bai wuce dan abin da ya saura na kwanakin Ramadan ba.

Saura kwana nawa ne? Muna shirin shiga goma na karshe, kwanakin da Annabinku (S.A.W) yake matukar zage damtse domin bauta wa Allah.

A ashirin na farko yana hada sauran ibadoji da Sallah da barci, amma da goman karshe ya shigo, sai ya tattara shimfidarsa ya daure mazagin wadonsa, ya kaurace wa shimfidar barcinsa, ya tashi iyalansa ya kwankwasa kofar Fatima da Aliyu (Allah Ya yarda da su) yana mai cewa: “Ashe ba za ku tashi ku yi Sallah ba?”

Sannan ya fuskanci dakunan matansa yana umarni tare da bayyana cewa: “Ku farka Ma’abota Babban Gida (Ahlul Bait), da yawa masu sutura a duniya tsirara suke a Lahira.”

Annabi (S.A.W) ya kasance idan goman karshe na Ramadan ya zo, ba ya barin duk wanda zai iya tsayuwar dare daga cikin iyalinsa a kwance face ya tashe shi.

Kuma magabatan kwarai sun fi sauran mutane bibiya da koyi da Annabi (S.A.W).

Ya zo a cikin Muwadda na Imam Malik (Allah Ya yi masa rahama) cewa Umar dan Khaddabi (RA) ya kasance yana Sallah gwargwadon yadda Allah Ya so, har sai dare ya raba, sai ya tashi iyalansa yana ce musu “Sallah! Sallah!”

Sannan sai ya karanto wannan aya: “Ka umarci iyalinka da yin Sallah da hakuri a kanta. Ba Mu tambayarka dukiya, Mu ne masu azurta ka, kuma kyakkyawan karshe na masu taƙawa ne.”

Sufyanu Suri (Rahimahullah) ya ce, “An so idan goma karshe ya shigo (Musulmi) ya yi kokari da daddare ya yi kokari a cikinsa, ya tashi iyalinsa da ’ya’yansa su yi Sallah matukar za su iya hakan.”

Wata mata daga cikin magabatan kwarai ta fada wa mijinta cewa: “Hakika dare ya tafi alhali akwai doguwar tafiya a gabanmu, sannan guzirinmu kadan ne, kuma ayarin salihai ya yi mana nisa, mu ne muka saura a hanya!”

Ya ku Musulmi! Ku san darajar zamaninku, ku girmama mafi falalar lokacinku, ku gabatar da aikin alheri domin kanku.

Kada ku bata lokacinku a cikin abin da ba neman kusanci ba ne ga Allah. Ba da buri ake kyautata zaton alheri ba, ana kyautata zato ne da kyautata aiki.

Sanya ran samun rahama tare da aikata sabo wani nau’i ne na wauta da tabewa. Ba da kuka da share hawaye ake tsoron Allah ba, ana tsoron Allah ne ta barin abin da ake tsoron ukuba a kansa.

Ya ku masoya! Ku gabatar da aikin alheri ga kanku, ku tsayu kuma ku yi kankan da kai.

Uwar Muminai A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “Ya Manzon Allah! Shin idan na riski daren Lailatu Kadari me zan ce a cikinsa?

Sai ya ce: “Ki ce: “Allahumma innaka afuwun tuhibbul afuwa, fa’afu anni.”

Ma’ana “Ya Ubangiji! Kai Mai yawan afuwa ne, Kana son afuwa, Ka yi min afuwa.” Ku yawaita wannan addu’a a cikin goman karshe.

Ubangijinku Ya ce, “Idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni, to, lallai ne Ni ina kusa, Ina amsa kiran wanda ya yi kira idan ya kira Ni.

“Don haka su amsa Min, kuma su yi imani da Ni, tsamaninsu suna shiryuwa.”

Ko kun san su wane ne wadannan bayi? Halittu dukkansu bayin Allah ne, sai dai kuma wadannan bayi kebantattu ne.

Su ne bayi daga ma’abuta addu’a, bayin da suke jirar a amsa musu, su ne masu addu’a cikin kankan da kai, masu addu’a tare da babbar fata, masu kankan da kai wajen kwadayin amsawa; “Idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni, to, lallai Ni ina kusa…”

Lallai addu’a tana da wani sha’ani mai ban-mamaki da tasiri babba wajen kyawun karshe da gyara hali da dukiya da dacewa a cikin ayyuka da albarka a cikin arziki.

Shin ba ku ganin wanda ya dace da rabo ta wajen addu’a, yana samun rabonsa daga kankan da kai da fakewa ne a wurin Allah a kowane hali ba?

Shi ne yake komawa ga Allah a dukkan bukatunsa ya yi addu’a, a yi masa addu’a, ya rabauta da addu’arsa ta kashin kansa da ta waninsa.

Mahaifansa suna son sa, ’ya’yansa suna yi masa da’a, mutanen da suke kusa da shi dukkansu suna kewaye shi da addu’a.

Mahaliccinsa Yana son sa, don haka Ya fawwala karba masa. Sai halayensa su kyautata, aikinsa ya yi kyau, hannuwa su dagu sama, harsuna su daukaka wajen yi masa addu’a.

Allah Yana lura da shi Ya datar da shi, sha’aninsa yana kyautatuwa tare da dacewa.

Yaya za a kwatanta shi da wanda aka haramta masa haka, wulakatacce wanda bai dandani zakin ganawa da Ubangijinsa a Ramadan ba?

Yaya za a hada shi da wanda ya ji kunyar bauta wa Ubangijinsa, ya yi girman kai daga rokon Ubangijinsa? Abin haramtawa da ya rufe kofar rahama ga kansa, ya lulluba da tufar gafala?

Hudubar Juma’a daga Muhammad bin Mabrouk Lu’awani, Masallacin Khalid bin Walid da ke Saudiyya

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Goman Karshe Rahama Ramadan Wa azi

এছাড়াও পড়ুন:

Nazarin CGTN: Fahimtar Matsayin Sin Cikin Yanayin Tattalin Arzikin Duniya Na Da Muhimmanci

Tafarkin samun ci gaba mai karfi da inganci, da karuwar kuzarin kirkire-kirkire da ci gaba da fadada bude kofa, su ne suka hadu suka samar da wani sabon matsayi ga tattalin arzikin kasar Sin a taswirar tattalin arzikin duniya. Ci gaba mai inganci da fadada bude kofa, ba muhimman jigon ne dake ingiza tattalin arzikin Sin kadai ba, har da nuna yanayin sauyawar abubuwan dake haifar da ci gaba a duniya. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar ta kafar intanet, ya nuna yadda masu bayar da amsa daga fadin duniya suka yi imanin cewa, tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba ta kowace fuska ba tare da tangarda ba, lamarin da ya samar da tabbaci ga tattalin arzikin duniya.

Karfin tattalin arzikin Sin ya dagora ne da sabon karfin samar da hajoji da hidimomi da ke samun ci gaba cikin sauri, wadda ake ganin saurin ci gabanta ta hanyar kirkire-kirkire. Nazarin ya nuna cewa, kaso 93.6 na wadanda suka bayar da amsa, sun yi imanin cewa, kirkire-kirkire na taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki mai inganci na Sin. Wasu kaso 96.6 kuma sun yi imanin cewa, kasar Sin na jagorantar manyan sauye-sauye a tsare-tsaren tafiyar da masana’antu da na tattalin arziki ta hanyar kirkire kirkiren kimiyya da fasaha.

A matsayinta na kasa ta biyu mafi yawan masu sayayya, kasar Sin ce ke da mutane masu matsakaicin kudin shiga mafi yawa a duniya, inda take da gagarumin karfin sayayya da na zuba jari. Nazarin ya nuna cewa, kaso 82.3 na masu bayar da amsu sun yi imanin cewa, kamfanonin kasashen waje za su iya amfani da fa’idojin da suke da shi wajen shiga kasuwar kasar Sin domin kara samun karfin takara a duniya. (FMM)

ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kamfanin CRCC Ya Kammala Shimfida Hanyar Jirgin Kasa A Gadar Layin Dogo Mafi Tsawo A Afrika Dake Algeria December 11, 2025 Daga Birnin Sin Yadda Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samar Da Karin Damammaki Ga Kasashe Masu Tasowa December 11, 2025 Daga Birnin Sin Kamfanonin Sin Sun Kera Tare Da Sayar Da Motoci Sama Da Miliyan 31 Tsakanin Janairu Zuwa Nuwamban Bana December 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta soki Kasashe Masu Karfi Na Bawa Isra’ila Dama Ta Musamman Wajen Kai Hare-hare
  • Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina
  • Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
  • Nazarin CGTN: Fahimtar Matsayin Sin Cikin Yanayin Tattalin Arzikin Duniya Na Da Muhimmanci
  • Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman
  • Yadda za ku cike neman aikin dan sandan Najeriya na 2025/2026
  • An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara
  • Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa
  • Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya
  • Saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya soya qwaqwalwarta