Gobara ta kashe yara 3, ta jikkata 13 a Yobe
Published: 19th, March 2025 GMT
Rahotanni sun nuna cewa gobara ta kashe yara uku tare da jikkata wasu 13 a ƙauyuka tara na Jihar Yobe, tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin 2025.
Gobarar ta kuma lalata gidaje 86, inda ta bar mutane da dama ba tare da matsuguni ba.
Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas Ba tarbiyya nake koyarwa ba — Sadiq Sani SadiqBabban sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Yobe (YOSEMA), Dokta Mohammed Goje, ya bayyana cewa rashin kula da wutar lantarki, amfani da gas, ƙonewar daji, da kuma zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba, ke haddasa yawan gobara a jihar.
Ya ce lamarin ya fi shafar yankunan Damaturu, Gulani, da Yusufari, inda mazauna ke kokawa kan asarar da suka yi.
Domin magance matsalar, hukumar YOSEMA ta fara wayar da kan jama’a kan hanyoyin kauce wa gobara.
Haka kuma, sun kafa kwamitoci da za su taimaka wajen kare lafiyar al’umma, musamman a lokacin rani da hunturu.
Dokta Goje ya ce hukumar, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta jihar, za su ɗauki matakan hana ƙone daji da kuma bin ƙa’idojin zubar da shara domin rage haɗuran gobara.
A gefe guda, Gwamna Mai Mala Buni ya umarci hukumar YOSEMA da ta tantance ɓarnar da gobarar ta yi, domin sanin irin taimakon da waɗanda lamarin ya shafa suke buƙata.
Gwamnan ya tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa za a tallafa musu.
A halin yanzu, hukumomi na ci gaba da faɗakar da jama’a kan muhimmancin kiyaye dokokin kare gobara domin gujewa aukuwar irin wannan iftila’i a gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara gwamnati rasuwa shara yara
এছাড়াও পড়ুন:
EFCC ta tsare Malami kan binciken kuɗaɗen Abacha
Hukumar EFCC ta tsare tsohon Antoni-Janar na Tarayya, Abubakar Malami, saboda binciken da ya shafi dawo da wani ɓangare na kuɗaɗen Abacha.
Hukumar ta kira Malami a makon da ya gabata, inda ta yi masa tambayoyi kan wani bincike da ta ke inda ta sake shi daga bisani, amma yanzu ta tsare shi.
Real Madrid za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da tsaroMalami ya ce bai aikata komai ba, kuma ba shi da alaƙa da abin da ake zargi.
A cikin wata sanarwa, ya ce: “Ba a taɓa zargina, gayyata ko bincikena game da tallafa wa ta’addanci ba. Duk wani yunƙuri na danganta ni da irin wannan laifi ƙarya ne.”
Ya ƙara da cewa rahotannin kafofin yaɗa labarai ke watsawa sun yi masa mummunar fassara.
“Ba daidai ba ne a ce aikina na gwamnati ya zama hujja ta tallafa wa ta’addanci. A lokacin aikina, na yi aiki tuƙuru wajen ƙarfafa yaƙi da ta’addanci, ba goyon bayansa ba.”
EFCC ba ta fitar da wata sanarwa kan tsare Malami ba.
Haka kuma bai wallafa komai a shafukan sada zumunta ba tsawon kwanaki huɗu.