Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas
Published: 19th, March 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin Mai Kula da Jihar Ribas.
An rantsar da shi ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba.
Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin RibasNaɗin ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Talata, bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin Jihar.
Bayan ayyana dokar ta-ɓacin, Tinubu ya sanar da cewa Vice Admiral Ibas ne zai jagoranci jihar na tsawon watanni shida.
Yayin jawabinsa, Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa dokar ta-ɓacin ba ta shafi ɓangaren shari’a ba, kuma kotuna za su ci gaba da gudanar da aikinsu kamar yadda doka ta tanada.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dokar Ta Ɓaci Fubara
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta sake hana PDP gudanar da babban taronta na ƙasa
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sake hana jam’iyyar PDP gudanar da babban taronta na ƙasa da ta ke shirin yi.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Peter Odo Lifu, ya yanke hukuncin ne a ranar Juma’a.
Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPPYa ce taron da aka tsara yi a Ibadan a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba ba za a gudanar ba sai an bai wa tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, damar sayen fom ɗin takarar kujerar shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Alƙalin ya kuma umarci INEC da kada ta sanya baki ko ido a kan taron har sai an bai wa Lamido damar sayen fom.
Lifu, ya ce PDP dole ta bi dokokinta ta kuma bai wa duk ’ya’yan jam’iyyar waɗanda suka cancanta damar yin takara.
Ya ce ba daidai ba ne a hana Lamido sayen fom ɗin takara.
Lamido, ya garzaya kotu ne bayan hana shi sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar.
Alƙalin ya ƙara da cewa PDP ba ta fitar da sanarwar da doka ta tanada ba, kuma ba ta bayar da kwanaki 21 na sanarwa kafin gudanar da taron kamar yadda yake a tsarinta.