Ɗan Afirka da yake da ‘ya’ya 104 da jikoki 144
Published: 19th, March 2025 GMT
Mzee Ernesto Muinuchi Kapinga, wani mutum ne daga wani karamin kauye a Tanzaniya, wanda yake da iyali na musamman.
Ya auri mata 16, yana da ’ya’ya sama da 100 da jikoki 144.
A kwanakin nan, maza da yawa suna ta kokarin samun iyali da neman haihuwa, duk da ana kallon karuwar iyali kamar karin matsin rayuwa ne mai yawa.
Kula da yara sama da biyu ko uku abu ne da ba za a yi tsammani ba ga galibin matasa, amma kuma akwai maza irin su Mzee Ernesto Muinuchi Kapinga wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen fadada iyalansu gwargwadon iko.
Mutumin ɗan asalin wani ƙaramin ƙauye ne da ke Njombe a kasar Tanzaniya, a halin yanzu yana da mata 16, ‘ya’ya 104 da jikoki 144.
Gidansa kamar wani dan karamin kauye ne, inda kowace mace daga cikin matansa take da bangarenta kuma iyalansa suna yawo a ko’ina, suna gudanar da sana’o’i, suna kula da dimbin yara.
A wata hira da ya yi da Afrimax kwanan nan, Ernesto Kapinga ya ce, ya fara fadada iyalinsa ne bisa bukatar mahaifinsa.
Ya auri matarsa ta farko a shekara ta 1961, kuma ya haifi da na farko bayan shekara guda, amma mahaifinsa ya gaya masa cewa, mace daya ba ta isa ba.
Sai ya ce zai ba shi sadaki idan ya amince ya auri karin mata don ya samu haihuwar yara da yawa.
“Danginmu ba su da yawa, ina so ka fadada su,” mahaifin Kapinga ya fada masa, kuma ya amince da hakan.
Mahaifinsa ya biya sadakin matansa biyar na farko, amma bai tsaya nan ba. A ƙarshe Ernesto ya auri mata 20.
Wasu sun zabi barinsa a wani lokaci, wasu kuma sun rasu, amma yau yana zaune da mata 16, bakwai daga cikinsu masu kananan shekaru ne.
Matan Mzee Ernesto Muinuchi Kapinga sun bayyana cewa, ya kasance miji na gari.
Ɗaya daga cikin matansa ta bayyana wa ’yar’uwarsa irin kyakkyawar rayuwar da take yi tare da shi, don haka suka yanke shawarar zama da shi.
“A nan, kowa yana da rawar da yake takawa,” in ji magidancin.
“Kowace mace tana da gidanta da kicin dinta, babu gasa a tsakaninsu.
“Kowacce ta san wurinta, tare muke noma, muna ci tare, muna aiki tare .
“Wannan ba gida ba ne kawai, tsari ne da ake bi kuma yana aiki.
“To ta yaya mutum zai samar da daruruwan daruwan mutane abincin da za su ci?.
To a fili yake cewa, dukakan iyali suna dogara ne da aikinsu don samun abinci, kuma sun dogara kacokan ga amfanin gonakinsu da dabbobinsu wajen samun abinci.
Suna shuka masara da wake da rogo da ayaba, kuma abin da ya yi rara, sukan yi kasuwancinsa.
“Mutane suna tunanin ina sarrafa komai,” in ji Kapinga.
“Amma gaskiyar magana ita ce, matana suna hada kan wannan iyali, ni kawai ina yi musu jagoranci ne.”
Matan sun bayyana cewa, a koyaushe suna bayyana matsalolinsu kuma ba sa barin fushi ya yi barazana ga hadin kan gida.
Idan ba za su iya daidaita al’amura a tsakaninsu ba, sai su kawo al’amura ga Ernesto kuma ya saurare su, ba ya goyon bayan wani bangare, amma yana ba su shawara kawai.
A bayyane yake, wannan tsarin iyalin yana aiki daidai ya zuwa yanzu.
Wani abin sha’awa shi ne, Mzee Ernesto Muinuchi Kapinga ya yarda cewa, a wasu lokuta yakan manta sunayen ‘ya’yansa da jikokinsa, yana mai cewa yakan tuna sunayensu 50 daga cikinsu. Ya ce yakan tuna sauran idan ya ga fuskokinsu.
Iyalan Kapinga sun kasance babban dangin da ya fi girma, amma ya rasa yara 40 sakamakon rashin lafiya da hadura.
Yana bakin ciki idan ya tuna da su, amma ya ci gaba da rayuwarsa don yana da ‘ya’ya da yawa a raye wadanda ke bukatar kulawarsa koyaushe.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Na Iran Ya Ce: Maganar ‘Yan Sahayoniyya Rudu Ne Maras Amfani
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin wuta da zai iya janyo tashin gobara da zai iya kona yankin gaba daya.
A jawabin da ya gabatar yayin taron kolin majalisar shawarar Musulunci ta Iran a yau Talata, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Firai ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya mai laifi ne mai zubar da jinin fararen hula, saboda neman hana mutuwarsa a fagen siyasa, kuma yanzu yana yin barazana ga al’ummar Iran mai girma. Qalibaf ya yi nuni da cewa, wannan mutum mai rauni yana son canza haryar tafiyarsa a kullum rana saboda tsoron kada a kama shi sakamakon kasancewarsa mai laifi da yafi zama abin ki a tarihin wannan zamani.
Qalibaf ya kara da cewa; Bayan shafe shekaru da dama Netanyahu yana yaudarar kafafen yada labarai, a halin yanzu gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta fito fili kuma ta bayyana hakikanin fuskar wannan azzalumi ga duniya, musamman ga matasan Amurka da Turai. Qalibaf ya kara da cewa babu wani abin da wannan gwamnatin ta cimma sai kai hare-haren bama-bamai kan makarantu da asibitoci, kuma ba ta cimma burin da ta ayyana a farkon yakin ba, kuma halin da ake ciki yana da matukar rashin tabbas.