Aminiya:
2025-07-08@02:25:22 GMT

Dalilin da matan karkara a Kano suka fi son haihuwa a gida

Published: 8th, July 2025 GMT

‎Wata ƙungiya mai zaman kanta, Nigeria Health Watch ta ce ta gano har yanzu fiye da rabin matan da ke zaune a yankunan karkarar Jihar Kano sun fi son haihuwa a gida a maimakon zuwa asibiti.

‎Kungiyar ta alaƙanta hakan da al’adun mutanen, waɗanda ta ce an fi samun masu su a ƙauyuka da kuma yankunan karkara fiye da a birane.

‎Daraktar shirye-shirye ta ƙungiyar, Kemisola Agbaoye ce ta bayyana hakan ranar Litinin, yayin gabatar da rahoto a wani taron masu ruwa da tsaki don bayyana abubuwan da suka gano a binciken da suka gudanar a ƙananan hukumomi shida na jihar.

Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya Amurka za ta ɗauki nauyin ’yan tawaye domin yaƙi da ta’addanci

‎Ta ce taron zai taimaka wa gwamnati domin gano ɓangarorin da za ta fi mayar da hankali wajen magance matsalar mace-macen mata da ƙananan yara.

‎Kemisola ta ce, “Mun gano cewa akwai banbanci sosai tsakanin yankunan karkara da biranen da muka gudanar da bincikenmu.

“Alal misali, a wasu ƙananan hukumomi, mun gano cewa fiye da kaso 50 cikin 100 na mata masu juna-biyu har yanzu sun fi son haihuwa a gida, inda unguwar zoma ta gargajiya suke karɓar haihuwarsu.

‎“Hakan na faruwa ne duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na ganin ta rage mace-mace yayin haihuwa a Najeriya.

“ Matsalar mutuwar mata a wajen haihuwa babbar matsala ce a Najeriya, musamman a Kano, inda muka gano fiye da rabin mata sun fi so su haihu a gida. Wannan muhimmin bincike ne ga ƙoƙarin gwamnati a wannan bangare.

‎“Bugu da kari, akwai kuma wasu dalilai da muka gano suna ƙara ta’azzara wannan matsalar kamar su rashin kyan hanyoyi da ma kuɗin zuwa asibiti ga matan, da kuma al’adun mutanen,” in ji Daraktar.

‎Ta kuma ce ƙungiyar tasu na bayar da shawarar ƙara mayar da hankali wajen wayar da kan mutane domin canza tunaninsu su rungumi haihuwa a asibiti.

‎Kemisola ta kuma ce taron wani ɓangare ne na shirin gangaminsu na ƙasa da ƙasa, wanda ke taimaka wa gwamnatin jihar Kano ta magance matsalolin da ke damun asibitocin sha-ka-tafi.

‎A nasa ɓangaren, Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce yanzu haka jihar na kan aikin gina asibitocin sha-ka-tafi guda 260 a faɗin jihar, kuma tana shirin kammalawa tare da buɗe su nan da shekara mai zuwa.

‎Ya ce shirin wani ɓangare ne na ƙudurin gwamnatin jihar na ganin ta gina aƙalla ƙaramin asibiti a dukkan gundumomi 484 da ke jihar.

‎Kwamishinan ya kuma ce har ila yau, jihar na aikin ɗaga likafar ƙananan asibitoci 18 zuwa matsakaita a ƙoƙarinsu na ganin kowacce ƙaramar hukuma a jihar na da matsakaicin asibiti.

‎“Game da batun mata masu haihuwa a gida kuwa, matsala ce da ta wuce gina asibitoci ko samar musu da kayan aiki, magana ce ta canza tunanin mutanen.

“Yanzu haka akwai muhimmin aikin canza tunanin mutane ta hanyar amfani da masu riƙe da sarautun gargajiya da kuma kafafen yaɗa labarai wajen wayar da kan jama’a a kan illar haihuwa a gida da rashin zuwa asibiti,” in ji Kwamishinan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Haihuwa Jihar Kano haihuwa a gida

এছাড়াও পড়ুন:

Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya

Kananan yara uku sun rasu yayin da wasu da shidan ke kwance a asibiti sakamakon sake bullar cutar nan ta mashako a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.

Wani mazaunin unguwar Kwarbai a yankin na Zariya, Mallam Bashir Magaji wanda ya rasa ’yarsa sakamakon barkewar cutar wadda a turance ake kira Diphtheria, ya bayyana yadda take bazuwa cikin sauri a kwanakin nan.

Kira ga Haƙuri: A Dakatar da Ƙirƙirar Sabbin Masarautu a Jihar Bauchi Amurka za ta ɗauki nauyin ’yan tawaye domin yaƙi da ta’addanci

A cewarsa, ’yarsa da ta nuna alamun kamuwa da cutar na kumburin wuya da sarkewar numfashi, an gaggauta mika ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, amma daga bisani ta ce ga garinku nan.

Mallam Bashir ya bayyana cewa, tun bayar rasuwar ’yarsa, a yanzu haka an samu wasu karin yaran uku da suka soma nuna alamun kamuwa da cutar kamar dai yadda ta kasance ga ’yarsa.

Sai dai ya ce ya gaggauta kai rahoton lamarin ga wasu muhukuntan lafiya mafi kusa wadanda suka turo tawagar jamiai da ta soma bayar da allurar riga kafi a yankin.

“Na samu labarin cewa alamun cutar sun bayyana a jikin wasu yaran makwabcina biyu da wata mata a layin da nake zama.”

Ya kara da cewa an kwantar da wasu yaran hudu da su ma suka nuna alamun cutar a wata cibiyar lafiya ta Kakaki da ke kusa da Kwarbai, kuma tuni har an sallami yaro daya.

Ya kuma bayyana damuwa kan zargin cewa babu allurar rigakafin cutar a duk fadin Jihar Kaduna, “wadda na samu labarin cewa sai daga Jihar Neja aka kawo mana ita.”

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin sakatariyar lafiya ta Karamar Hukumar Zariya, amma ba ta amsa kiran da wakilinmu ya yi mata ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Asibiti Mai Zaman Kansa A Kano Zai Fara Aikin Manyan Tiyatu Tare Da Rage Kuɗi Kaso 50%
  • Asibiti Mai Zaman Kansa A Kano Zai Fara Manya Manyan Tiyatu Tare Da Rage Kuɗi Kaso 50%
  • Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya
  • Mutane 21 Suka Mutu A Hatsarin Mota A Hanyar Zaria Zuwa Kano
  • Gwamna Yusuf Ya Kaddamar Rabon Na’urorin Rarraba Lantarki 500
  • Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Tunisiya Da Ci 3-0 A Moroko
  • Muhimman Kamfanonin Jiragen Sama A Duniya Sun Farfado Da Zirga-Zirgaf Zuwa Iran
  • Gonakin Koko: Mata sun yi barazanar zanga-zanga tsirara a Kuros Riba
  • Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a Kano