Leadership News Hausa:
2025-11-14@21:43:03 GMT

Nijar Ta Fice Daga Kungiyar Kasashen Da Ke Amfani Da da Faransanci

Published: 18th, March 2025 GMT

Nijar Ta Fice Daga Kungiyar Kasashen Da Ke Amfani Da da Faransanci

Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, Nijar na ci gaba da janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya.

A baya-bayan nan ma, tare da Mali da Burkin Faso, ƙasar ta fice daga ƙungiyar ECOWAS.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku.

Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Faransanci Kungiya Nijar

এছাড়াও পড়ুন:

Yahudawa sun banka wa masallaci wuta a Yammacin Kogin Jodan

Wasu Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna sun lalata tare da kona wani masallaci da ke gabar yammacin kogin Jodan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda kamfanin dillancin Labarai na Falasɗinu (WAFA) ya ruwaito a ranar Alhamis.

WAFA ya ce Yahudawan sun kuma yi rubuce-rubucen batanci a bangon masallacin da ke cikin wani ƙauye a arewa maso yammacin yankin, da safiyar ranar.

HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani

Wasu kafafen yaɗa labarai kuma sun ce rubuce-rubucen da aka fesa da fenti sun haɗa da cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW) da harshen Ibrananci.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana gudanar da bincike kan zargin.

Babu rahoton rauni ko mutuwa a lamarin kawo yanzu, amma bidiyon da ke yawo a kafafen yada labaran Falasɗinu da Isra’ila sun nuna lalacewar masallacin.

Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya bayyana harin a matsayin “mai matuƙar daure kai.”

Herzog ya ce wannan laifin da “ƙalilan daga cikin masu laifi” suka aikata ya “saba ka’ida,” inda ya ƙara da cewa “dukkan hukumomin gwamnati dole su ɗauki mataki mai ƙarfi don kawar da wannan dabi’a.”

Babban hafsan sojin Isra’ila, Laftanar Janar Eyal Zamir, ya goyi bayan suka da Herzog ya yi, yana mai cewa rundunar soji “ba za ta lamunci ayyukan wasu ’yan ƙalilan masu laifi da ke bata sunan jama’ar da ke bin doka ba.”

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya (UN), Antonio Guterres, a ranar Alhamis, ya la’anci harin da Yahudawan masu haramtattun gidajen suka kai kan masallaci a yankin wanda Isra’ila ta mamaye.

Tashin hankali daga Yahudawa masu ra’ayin rikau kan Falasɗinawa a yankin ya ƙaru tun bayan fara yaƙin Gaza a watan Oktoban 2023, wanda aka fara bayan hare-haren da Hamas ta jagoranta kan Isra’ila.

Tun daga lokacin, an samu ƙaruwar hare-haren da ke haddasa mutuwa tsakanin Falasɗinawa da sojojin Isra’ila a yankin na Yammacin Kogin na Jodan.

Rundunar sojin Isra’ila na yawan fuskantar zargi kan gazawarta wajen ɗaukar mataki mai ƙarfi kan tashin hankalin da Yahudawa ke haddasawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza
  • Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati
  • Yahudawa sun banka wa masallaci wuta a Yammacin Kogin Jodan
  • Xi Ya Bukaci Matasa Masanan Harkokin Sin Su Kasance Gada Tsakanin Sin Da Duniya
  • Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe
  • MURIC ta buƙaci Tinubu ya sauke Amupitan daga shugabancin INEC
  • Iran Ta Zama Memba A Kungiyar Tattara Bayanai Na  Ilimomi Da Kere-kere Ta Duniya ( ISKO)
  • Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP
  • Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP
  • Kungiyar Wamban Shinkafi Ta Amince Da Tinubu a 2027