Aminiya:
2025-06-23@09:49:29 GMT

Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗin 2025 na N54.99trn

Published: 1st, March 2025 GMT

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da ya kai Naira tiriliyan 54.99.

A ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025, Majalisar Dokoki ta amince da kasafin bayan tattaunawa da nazari a kansa.

Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano Gwamnatin Sakkwato ta nemi malaman Jami’a su janye yajin aiki 

A baya dai, Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin da ya kai Naira tiriliyan 49.

7, amma daga bisani aka ƙara adadin kuɗin.

Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin a ranar Juma’a, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Kasafin kuɗin na 2025 ya ninka wanda aka yi a bara, wanda ya tsaya a Naira tiriliyan 27.5, da ƙarin kashi 99.96 cikin 100.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila

Iran ta lalata cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, wato cibiyar kimiyya ta Weizmann Institute of Science da ke birnin Tel Aviv.

Cibiyar, wadda ke da alaƙa da binciken harkokin sojin Isra’ila, ta sanar da cewa harin da Iran ta kawo ɗin ya yi sanadiyar ɓarnar da ta kai kimanin Dala miliyan 500.

Makaman Iran sun lalata gine-gine da dama a cibiyar, lamarin da ya sanya masu bincike faɗi-tashi don ceto samfurin bincike a cikin ɓaraguzan gini, a yayin da gobarar ke ci.

Wani makami mai linzami ya tarwatsa wani gini mai ɗauke da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani da dama, a yayin harin na ramuwar gayya, bayan da Isra’ila ta kashe masana kimiyyar nukiliya na Iran.

2027: Manyan ’Yan adawa na neman rajistar sabuwar jam’iyya Wani ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 71 a Akwa Ibom

Makamin ya faɗo kan cibiyar ne kafin wayewar garin ranar Lahadi, amma babu wanda ya ji rauni domin cibiyar ba kowa a cikinta a lokacin.

Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ziyarci wurin, inda ya ce, “wannan harin ne dalilin da ya sa Isra’ila ba za a taɓa barin Iran ta mallaki makaman nukiliya ba.”

Idan ba a manta ba, Isra’ila ce ta fara kai hari kan Iran a ranar 13 ga Yuni, bisa hujjar cewa abokiyar gabar tata tana dab da ƙera makaman nukiliya.

Iran, wadda ta dage cewa shirin nukiliyarta don dalilai na zaman lafiya ne kawai, ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa a kan Isra’ila.

Hare-haren Isra’ila sun yi sanadiyar mutuwar wasu manyan masana kimiyyar nukiliya na Iran, da manyan shugabannin sojojin Iran, da fararen hula tare da lalata gidaje da tashoshin nukiliya da ababen more rayuwa.

Duk da cewa yawancin binciken cibiyar Weizmann sun danganci fannin gas magunguna da ilimin kimiyya ne, amma tana kuma da alaka da tsaro.

A watan Oktoba na 2024, ta sanar da haɗin gwiwa da babban kamfanin tsaro na Isra’ila, Elbit, kan “kayayyakin da aka samo daga halittu don aikace-aikacen tsaro.”

Cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, tana da ƙungiyoyin bincike 286, masana kimiyya ma’aikata 191, da daruruwan dalibai.

Iran ta sanar a ranar Juma’a cewa ba za ta tattauna makomar shirin nukiliyarta ba yayin da take fama da hare-hare daga Isra’ila.

Duk ƙoƙarin ƙasashen Turai na jan hankalin Tehran zuwa tattaunawa bai nuna alamun nasara ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hajji 2025: Kashi Na Farko Na Alhazan Abuja Sun Dawo Gida Nijeriya
  • Tinubu Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Bam A Borno, Ya Yi Alhinin Fashewar Wani A Kano
  • EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Kamfanoni Biyu Gaban Kuliya Bisa Damfarar Naira Miliyan 80
  • Ƴansanda Sun Gargaɗi Masu Lalata Fastar Tinubu A Kano
  • Hajjin Bana: Jihohi 11 Sun Kashe Naira Biliyan 6.2 Kan Mahajjata
  • Yadda Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila
  • Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila
  • Duk Da Jihohin Nijeriya Sun Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashi Na 70,000, Ana Ci Gaba Da Fuskantar Matsin Rayuwa
  • Ɗan TikTok Tsulange Ya Shiga Hannu Bisa Wanka Da Rigar Mama A Titi
  • GORON JUMA’A 20-06-2025