Aminiya:
2025-08-02@11:46:42 GMT

Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya rasu

Published: 6th, March 2025 GMT

Allah Ya yi wa babban malamin Musulunci a Najeriya Sheikh Sa’idu Hassan Jingir rasuwa, bayan fama da rashin lafiya.

Marigayi Sheikh Sa’idu Hassan Jingir shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na II na Ƙasa Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bida Wa Iqamatis Sunan (JIBWIS).

Ana sa rana gudanar jana’izarsa da misalin ƙarfe biyu 2:00 na rana a Masallacin Santa, Unguwar Rimi cikin birnin Jos.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastan Da Shekara Ɗaya

Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin shekara guda ga shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi.

Kafin wannan ƙarin wa’adin, aikin Adeniyi zai kare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025. Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis ta ce wannan mataki na Tinubu zai ba Adeniyi damar kammala muhimman gyare-gyare da ayyuka da gwamnatin ke aiwatarwa a hukumar.

Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje

A cikin manyan ayyukan da ake son a kammala akwai shigar da cigaban zamani da ake yi wa hukumar Kwastan, da aiwatar da tsarin “National Single Window Project” da kuma cika alƙawuran Nijeriya a ƙarƙashin yarjejeniyar cinikayyar Afrika (AfCFTA).

“Tinubu Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastan Da Shekara Ɗaya” in ji sanarwar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya  
  • Kasar Slovenia Da Haramta Tura Makamai Zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • GORON JUMA’A 01-07-2025
  • Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya
  • Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu
  • Tinubu Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastan Da Shekara Ɗaya
  • Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam
  • Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar Kwastam
  • Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa
  • Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu