An samu cece-ku-ce a Jihar Sakkwato bayan da wata jita-jita ta yaɗu cewa Mataimakin Gwamnan jihar, ya karɓi shanu 400 da aka tanadar domin tallafa wa marasa galihu domin yin layya a lokacin Sallah Babba.

An ce shanun wata ƙungiya ce daga ƙasar Turkiyya ta bayar da su, ta hannun Hukumar Zakka da Waƙafi ta jihar, domin tallafa wa waɗanda ba su da halin yin layya.

Iran ta kai sabbin hare-hare birnin Tel Aviv da Haifa An tallafa wa mata 250 da abinci da kayan sana’a a Kaduna

Sai dai an zargi Mataimakin Gwamnan da karɓe su don amfanin kansa.

Wannan batu ya jawo jama’a a jihar suk dinga bayyana ra’ayoyinsu, inda wasu ke zargin an fifita jami’an gwamnati fiye da talakawa da aka yi nufin bai qa shanun.

Wasu sun zargi cewa malamai, limamai, ‘yan siyasa da ƙungiyoyin addini ne suka fi cin moriyar shanun.

Sai dai a wata hira da wakilinmu ya yi, da mataimakin gwamnan ya musanta karɓar shanun.

Ya ce: “Hukumar Zakka ce ke raba wa ’yan gudun hijira da ke fama da matsalar tsaro kamar a Sabon Birni da Isa.

“A shekarar da ta gabata sun karɓi shanu 20 kowane. Haka nan Illela da Gwadabawa sun samu goma-goma.”

Ya ƙara da cewa ba shi da hannu kai-tsaye, domin an tuntuɓar shi ne kawai a matsayin wanda zai jagoranci rarraba shanun ga jama’ar yankin da ke ƙarƙashinsa.

Shugaban Hukumar Zakka da Waƙafi ta jihar, Malam Muhammad Lawal Maidoki, ya ƙara bayyana cewa:

“Mataimakin gwamna bai karɓi shanun ba. An kafa kwamiti ƙarƙashinsa domin kula da rabon a yankin Gabas da ke fama da matsalar tsaro. Shanun sun ƙare kafin a gama rabawa. An ware 150, amma 106 ne aka samu.”

Ya kuma bayyana cewa sun yi niyyar yanka shanu 4,500 amma saboda wasu matsaloli, ciki har da rashin samun dabbobi da suka cika sharuɗan layya, sun yanka 3,000 kacal.

Malam Maidoki ya nemi afuwa ga duk wanda bai samu shanun ba, da waɗanda aka saba bai wa amma aka kasa ba su, da waɗanda suke tsammanin samun amma ba su samu ba.

Ya ƙara da cewa sun rubuta sunayen waɗanda ba su samu ba domin tunawa da su a shekara mai zuwa.

“Muna fata Allah Ya kawo mu wata shekara cikin lafiya da dama don ci gaba da tallafa wa marasa ƙarfi a irin wannan lokaci,” in ji shi.

A cewar hukumar, shirin ya laƙume sama da Naira biliyan ɗaya, kuma an raba naman layya ga dubban mutane da ba su samu damar yin yanka ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hukumar Zakka mataimakin gwamna Sakkwato zargi Hukumar Zakka

এছাড়াও পড়ুন:

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu

Kafin ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Barde ya taɓa zama Shugaban riƙo na Karamar Hukumar Wamba a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu
  • Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja