A Kasar Sudan Ta Kudu Jami’an Tsaro Sun Killace Gidan Mataimakin Shugaban Kasa
Published: 6th, March 2025 GMT
Kamfanin dillancin Labarun “Resuters” ya nakalto cewa jami’an tsaro sun killace gidan mataimakin shugaban kasa da wasu manyan jami’an soja da fararen hula.
Baya ga mataimakin shugaban kasa Riek Machar da sojoji su ka yi wa daurin talala a cikin gidansa, an kuma kama mataimakin hafsan hafsoshin sojan kasar Jamar Gabriel Doup Lam, sai kuma ministan man fetur Pout Kang Chol, haka nan kuma iyalansa da masu gadinsa.
Har ila yau a jiya Laraba an ga jami’an tsaro masu yawa sun killace ofishin mataimakin shugaban kasar, sai dai kuma wata majiyar ta ce, an gan shi ya isa wajen aikin nashi da safiyar jiya Laraba.
Wadannan matakan na tsaro dai sun biyo bayan fada mai tsanani da aka yi ne a tsakanin sojojin gwamnatin da kuma mayakan kabilar Nuwairah wacce mataimakin babban hafsan hafsoshin sojan kasar ya fito daga cikinta.
Gwamnatin shugaba Silva Kir tana tuhumar janar Doup Lam da cewa yana da hannu a tawayen ‘yan kalbilar tashi.
An sami asrar rayuka masu yawa a wannan fadan a tsakanin bangarorin biyu.
Shugaba Silva ya yi alkawalin cewa kasar ba za ta sake komawa cikin yaki ba.
A 2013 ne dai kasar ta Sudan Ta Kudu ta tsunduma cikin yakin basasa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen da sun kai 400,000 da kuma mayar da mutane miliyan 2.5 zama ‘yan gudun hijira.
Jumillar mutanen kasar da sun kai miliyan 11 suna fafutukar samun abinci da kuma ruwan sha mai tsafta. Sai dai daga baya na yi sulhu a tsakanin bangarorin biyu na shugaba Silva Kir da kuma mataimakinsa Riek Machar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin yankin.
Chen Binhua, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Larabar nan, ya ce kalaman Lai na cike da yaudarar kai, sun kuma fayyace manufar da ya dage a kanta ta “neman ’yancin kan Taiwan”. Kazalika, mummunan kayen da DPP ta sha a kuri’un da aka kada ranar Asabar din karshen makon jiya, ya fayyace ajandarta ta yin fito-na-fito da Sin, tare da fafutukar neman ’yancin kan Taiwan, matakin da ya yi hannun riga da ra’ayoyin al’ummun Taiwan, kuma zai fuskanci turjiya daga akasarin al’ummun yankin na Taiwan. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp