Matsin Tattalin Arziki Ya Karfafa Mana Gwiwar Raba Tallafi Ramadan – Sarkin Fada
Published: 6th, March 2025 GMT
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi.
Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna.
Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana cewa shirin rabon kayayyakin na daga cikin dabarun da kungiyar ta keyi na dakile tasirin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan.
Ya tabbatar da cewa sama da ‘yan uwa Musulmi dari da hamsin ne suka ci gajiyar shirin na watan Ramadan na bana, inda ya jaddada cewa su ma Kirista na kungiyar sun samu irin wannan tallafi a lokacin bukukuwan Kirsimeti na 2024.
Shugaban ya kuma yi kira ga mambobin kungiyar da su sake sadaukar da kansu wajen gudanar da ayyukansu domin ci gaban FRCN da kasa baki daya.
REL/MANSUR S PAKI
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Da za a kirkiri sabuwar jiha a Najeriya a yanzu, to da dole a samar da karin gwamna daya da sabuwar majalisar dokoki, da sababbin ma’aikatun gwamnati, da sauransu.
Samar da wadannan kuwa abu ne da yake bukatar makudan kudi – akalla Naira biliyan 30 duk shekara.
Ko da jihar za ta iya sama wa kanta kudin shiga kuma, za ta bukaci tallafi daga Gwamnatin Tarayya kafin ta tsaya da kafafunta.
Shin a halin matsin tattalin arzkin da take fuskanta yanzu, Najeriya tana da kudin da za ta reni sababbin jihohi kuwa?
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan abin da kirkirar sababbin jihohi a Najeriya yake nufi ta fuskar tattalin arziki.
Domin sauke shirin, latsa nan