PLA Reshen Kudancin Kasar Ta Yi Sintiri Na Hadin Gwiwa A Tekun Kudancin Sin
Published: 16th, June 2025 GMT
Kakakin yada labarai na rundunar sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin ko PLA reshen kudancin kasar, babban kanar na sojojin sama Tian Junli, ya bayyana cewa, jiya Asabar rundunar sojin ta gudanar da sintiri na hadin gwiwa a ruwan teku da kuma sama a yankin tekun kudancin Sin.
Tian ya kara da cewa, sitirin hadin gwiwa a teku da sama da Philippines ta gudanar tare da wasu kasashen duniya, ya kawo barazanar tsaro ga yankin tekun kudancin Sin, kuma ya lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali na yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar
Kasar Sin ta bullo da wani shirin bayar da tallafin kula da yara a fadin kasar wanda zai fara aiki daga shekarar 2025, a wani bangare na kokarin tallafa wa iyalai da kuma karfafa yawan haihuwa.
Shirin zai bai wa iyalai tallafin yuan 3,600, kimanin dalar Amurka 503, a kowace shekara a kan kowane yaro da bai kai shekaru uku da haihuwa ba.
Za a kebe tallafin daga cire harajin kudin shiga kuma ba za a kidaya shi a matsayin kudin shiga na iyalai ko na mutum daya ba a yayin da ake tantance masu karbar taimakon, inda abun zai zama kamar dai irin na wadanda ke karbar alawus na cin abinci ko kuma wadanda ke rayuwa cikin matsananciyar wahala. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp