IGP Ya Sake Bayar Da Umarnin Cafko Masa Mai Magana Da Yawun Gwamnan Kano Kan Bata Wa Ganduje
Published: 16th, June 2025 GMT
A cikin wata wasika mai kwanan wata 23 ga Mayu, 2025, mai lamba CR/3000/IGP-SEC/MU/ADM/14/ABJ/VOL 118/57, wacce aka aike wa sakataren gwamnatin jihar Kano, na cewa, IGP ya bukaci a mika Bature zuwa gaban wani jami’i, SP Mojirode B. Obisiji a ranar Alhamis 29 ga Mayu, 2025, domin amsa tambayoyi.
In ba a manta ba, IGP a watan Disamba, 2024 ya ba da irin wannan umarni tare da tura jami’an sa ido na IGP domin su kamo mai magana da yawun Gwamnan Kano tare da kai shi hedikwatar rundunar da ke Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Kammala Gyaran Makarantu Sama Da 1,200 A Kananan Hukumomi 44
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala gyaran makarantu fiye da 1,200 a kananan hukumomi 44 na jihar a wani yunkuri na farfado da harkar ilimi.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Ali Haruna Makoda, ne ya bayyana hakan yayin taron bitar yini guda kan kara kaimi a tsarin duba ingancin karatu, da aka gudanar a dakin taro na Cibiyar Kula da Ilimin Al’umma (CERC).
Ya ce banda gyaran manyan makarantu, gwamnatin ta ware Naira miliyan 484 domin gudanar da karin ayyukan gyare-gyare a gundumomi 484, inda kansilolin mazabu ke kula da gudanarwar ayyukan.
“A karo na farko a tarihin Kano ake aiwatar da manyan ayyukan ilimi a wannan mataki. Mun riga mun gyara makarantu sama da 1,200 kuma an fara ayyuka a matakin gundumomi.” In ji Dr. Makoda.
Kwamishinan ya kara da cewa wannan ci gaba yana cikin matakan aiwatar da dokar ta-baci da aka ayyana kan harkar ilimi a watan Mayun 2024, domin dawo da martabar fannin.
Ya ce gwamnatin ta kuma amince da Naira biliyan 3 domin gyaran makarantun kwana 13 na ’yan mata da gwamnatin da ta shude ta rufe.
Dr. Makoda ya bayyana cewa Kano na da fiye da makarantu 30,000, adadi mafi yawa a duk fadin Najeriya, kuma gwamnati na da niyyar ganin kowanne yaro ya samu ingantaccen ilimi cikin daidaito.
Taron ya horar da daraktoci, shugabannin makarantu da jami’an sa-ido, inda kwararru irin su Farfesa Ahmed Ilyasu da Bashir Sule suka gabatar da jawabai kan hanyoyin tantance darussa da dabarun inganta ilimi.
Daga Khadijah Aliyu