Rundunar Sojin Ruwa Ta Nijeriya Ta Lalata Haramtattun Matatun Mai 5 A Ribas
Published: 16th, June 2025 GMT
Aniaku ya bayyana cewa, an samu nasarar aikin yaki da satar danyen mai a yankin, ta hanyar amfani da bayanan sirri da NNS PATHFINDER ta samu kuma ta aiwatar cikin nasara.
Aniaku, ya kara nanata cewa, rundunar sojojin ruwan Nijeriya karkashin jagorancin babban hafsan hafsoshin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla, za ta ci gaba da jajircewa wajen yaki da satar danyen mai, wadanda ke haifar da babbar barazana ga tattalin arzikin kasar da kuma samar da makamashi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?
Shugabannin Rundunar tsaro da Tinubu ya sallama sun hada da shugaban rundunar tsaro ta kasa Janar Christopher Musa da shugaban sojojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla da shugaban sojojin sama Hassan Abubakar.
Wadanda suka maye gurbin su da idanu ya koma kan hobbasar kwazon da za su nuna su ne shugaban rundunar tsaro Olufemi Oluyede, shugaban sojojin kasa Waidi Shaibu, shugaban sojojin ruwa Idi Abbas da shugaban sojojin sama S.K Aneke sai kuma shugaban rundunar leken asiri, EAP Undiendeye wanda ya ci-gaba da rike kujerar sa.
Yan Nijeriya sun jima suna kukan duk da kwarewa da gogewar jami’an sojojin Nijeriya da irin makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro a kowace shekara amma matsalar kullum gaba- gaba take kara yi.
Yankuna da dama a Nijeriya musamman a Arewa- Maso- Yamma, Arewa- Maso- Gabas da Arewa ta tsakiya sun zama lahira kusa a bisa ga yadda barayin daji ke garkuwa da mutane, kone garuruwa da yi wa jama’a kisan kare dangi.
Gagarumar matsalar wadda tuni ta zama tamkar ruwan dare a tsayin shekaru ta ci dimbin rayuka da dukiyoyin al’umma ba adadi ba tare da samun gagarumar nasarar dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma ba.
Masana tsaro sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan sauye- sauyen. Wasu na ganin cewa sabbin jini za su iya kawo canji, yayin da wasu suka yi gargadin cewa sauya shugabanni kadai ba zai wadatar ba idan ba a yi gyaran tsari ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA