“Wannan shi ne karo na biyu, a shekarar da ta gabata dukkanin ƙananan hukumomi a Nijeriya ta hannun jihohinsu sun samu tallafin buhun shinkafa miliyan ɗaya mai nauyin kilogiram 10. Don haka, a wannan shekarar ma muna sake yin makamancin na bara.”

 

Hashim ya yi tilawar cewa gidauniyar Dangote ta himmatu wajen samar da tallafin kayan abinci ga mabuƙata, tallafi a ɓangaren kiwon lafiya, gina ɗakunan kwanan ɗalibai a jami’o’i, da sauran tallafi ciki har da wanda gidauniyar ta yi a lokacin annobar Korona.

 

Ya ce tallafin dafawa ne kan ƙoƙarin da gwamnatocin jihohi ke yi wa al’ummarsu, ya yi fatan cewa shinkafar da suka kawo Bauchi ɗin za ta je kai tsaye ga waɗanda aka bayar domin su wato marasa ƙarfi da marasa galihu a cikin al’umma.

 

Da ta ke amsar tallafin haɗi da ƙaddamar da rabarwa, Kwamishiniyar ma’aikatar kula da harkokin jin ƙai ta jihar, Hon. Hajara Yakubu Wanka ta nuna matuƙar godiyarsu ga gidauniyar Dangote bisa ga wannan tallafin.

 

Ta ce, a daidai lokacin da suke ƙoƙarin kammala rabon tallafin azumin da gwamnan jihar Bala Muhammad ke yi ne suka samu wannan tallafin daga wajen Dangote, don haka ne ta ce hakan zai ƙara kyautata jin daɗin jama’a a irin wannan watan da jama’a ke fama da azumi.

 

A cewar ta, cikin adadin buhu 25,000 da gidauniyar ta kawo Bauchi, za a rabar da guda 500 ga kowace ƙaramar hukuma daga cikin su 20, sai kuma guda dubu 10 da aka ware domin rabarwa a masallatai da cocina, gami da sauran guda 5,000 da za a rabar ga sauran masu ruwa da tsaki.

 

Shi ma a jawabinsa a madadin ƙananan hukumomin jihar Bauchi kuma shugaban ALGON na jihar, Hon. Mahmood Baba Ma’aji ya fara ne da gode wa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad a bisa tallafin da ya rabar ga ƙananan hukumomin jihar.

 

Hon. Ma’aji ya ce a satukan da suka wuce ne gwamnan ya ƙaddamar da rabon tallafin azumin wanda kowace ƙaramar hukuma sai da ta ci gajiyar hakan.

 

A gefe guda, ya gode wa gidauniyar Dangote bisa ƙara samar da tallafi a jihar ya bada tabbacin cewa za su sanya ido wajen rabon kayan tare da tabbatar da cewa a waɗanda suka dace su ci gajiyar tallafin ne suka amfana.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: gidauniyar Dangote

এছাড়াও পড়ুন:

Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka

A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya.

Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai cewa ma’aikatarsa “na shirye-shiryen ɗaukar mataki” bayan umarnin da Trump ya bayar.

Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 

“Muna shirye-shirye don ɗaukar mataki a Nijeriya. Idan gwamnatin Nijeriya ba ta kare Kiristoci ba, za mu kai hari, mu kawar da ‘yan ta’addan Musulmai da ke aikata wannan ta’asar,” in ji Hegseth.

Trump dai ya yi wannan barazanar ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a Truth Social, inda ya ce Amurka za ta dakatar da duk tallafin da take bai wa Nijeriya, kuma tana iya “shiga ƙasar da ƙarfin soji domin share ‘yan ta’addan da ke kashe Kiristoci.”

“Idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da duk wata tallafi, kuma mai yiwuwa ta shiga wannan ƙasar, ta cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’addan Musulmai masu zafin kishin addini,” in ji Trump.

Ya kuma gargaɗi gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta ɗaukar mataki, yana cewa idan Amurka ta kai farmaki “za ta yi shi cikin sauri, da tsananin ƙarfi, da gamsuwa.”

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan Trump ya mayar da Nijeriya cikin jerin ƙasashen da za a sanyawa ido, yana zargin cewa “ana yi wa Kiristoci kisan gilla” a hannun ƙungiyoyin Musulmi masu tsattsauran ra’ayi.

Sai dai a martanin da ya mayar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan addinai.

“Tun daga shekarar 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar ‘yan ƙasa daga addinai da yankuna daban-daban,” in ji Tinubu.

A cewar mai ba wa Tinubun shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, za a yi ganawa tsakanin Shugaba Tinubu da Shugaba Trump “a cikin kwanaki kaɗan masu zuwa” domin tattaunawa da warware wannan saɓanin fahimta.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Karamar Hukumar Bubura Ta Kai Tallafin Kayayyakin Abinci Cibiyar Gyaran Hali
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai