Sin Na Fatan Dukkan Bangarori Za Su Guji Daukar Mataki Da Zai Ta’azzara Rikici A Gaza
Published: 19th, March 2025 GMT
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yayin da take mayar da martani ga tambayar da wani dan jarida ya yi mata a taron manema labaru na yau 18 ga wata cewa, kasar Sin ta damu matuka kan halin da ake ciki a tsakanin Falasdinu da Isra’ila,kuma tana fatan dukkan bangarorin za su sa kaimi ga ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta yadda ya kamata, da kaucewa daukar duk wani mataki da zai ta’azzara lamarin, da hana afkuwar bala’in jin kai a mataki mai girma.
Hukumomin lafiya da ke Gaza sun ce adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai a wurare daban-daban a zirin Gaza da safiyar Talata ya kai 412. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Na’im Kassim: Ba Za Mu Taba Mika Makamanmu Ga Makiya Ba
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa; Batun makamin kungiyar ta Hizbullah na cikin gida ne, don haka ba za su taba mika makamansu ga abokan gaba HKI ba.
Sheikh Na’im Kassim Wanda ya gabatar da jawabi a jiya Laraba da dare a yayin tarukan Ashura, ya bayyana cewa; Ba za mu taba lamunta da a sa mu cikin kaskanci ba, ba kuma za mu mika kasarmu ba, ko kuma mu aminta da barazana daga wani mahaluki akan mu ja da baya.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Tattaunawar da ake yi akan makaman Hizbullah wani sha’ani ne na cikin gida, za kuma a warware batun ne a cikin gida, don ba shi da alaka da Isra’ila, ko kuma ta zama mai tsoma baki a tattaunawar da ake yi.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kara da cewa: Isra’ila ce, mai wuce gona da iri, kuma ta keta tsagaita wuta fiye da 3700,don haka wajibi ne a tilasta mata ta yi aiki da yarjejeniyar da ta kulla da gwamnatin Lebanon.”
Sheikh Na’im Kassim ya yi ishara da cewa; Isra’ila babbar barazana ce kuma hatsari ga musulmi, da kiristoci da kuma Yahudawa a Palasdinu, Lebanon, Masar, Syria, Jordan da wannan yankin da ma duniya baki daya.