Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji
Published: 18th, March 2025 GMT
Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji bayan ya tsallake karatu uku a wannan Talatar.
Wannan na zuwa ne bayan karatun tsanaki da majalisar ta yi ƙudirin a ranar Alhamis ta makon jiya.
Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansaAna iya tuna cewa, a makonnin bayan nan ne kwamitin kuɗi na majalisar ya gudanar da sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin, inda kuma ya tattara ra’ayoyin al’umma ya miƙa wa majalisar.
Dokar harajin da majalisar ta amince da ita ta ƙunshi ƙudiri guda huɗu da suka haɗa da ƙudirin dokar tafiyar da haraji da na kafa hukumar tattara haraji mai suna Nigeria Revenue Service da hukumar haɗaka ta tattara haraji da kuma ƙudirin haraji na Najeriya.
A watan Okotoban bara ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike da ƙudirin dokar ga majalisar dokokin ƙasar.
An dai shafe watanni ana taƙaddama kan dokar harajin wadda daga bisani gwamnonin jihohi 36 na Nijeriya suka cimma matsaya tare da amincewa da ƙudirin sabuwar dokar haraji, bayan gyare-gyaren da aka yi a kan rabon harajin kayayyaki na VAT da ya tayar da kura a ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dokar Haraji Majalisar Wakilai da ƙudirin dokar dokar haraji
এছাড়াও পড়ুন:
Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da burin da ya wuce na tara haraji tun yana Gwamna a Legas.
Adebayo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.
Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin NajeriyaA cewarsa, “Kowa ya san cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sananne ne wajen karbar haraji. Amma wannan tsarin karbar haraji ya fi tsarin da ya tarar da shi wanda ba shi da tsari.
“Ya yi hakan a Legas, sannan ya zo Abuja domin ya dora daga inda ya tsaya a Legas.”
Sai dai Adebayo ya ce Tinubu ya yi kokari wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
“A bayyane yake cewa tattalin arzikin da Shugaba Buhari ya bari ba a tafiyar da shi yadda ya kamata ba, kuma yana cikin mawuyacin yanayi kamar na mara lafiya da aka kai dakin jinya. Kamar yadda likita ke bukatar yin cikakken bincike domin gano matsalar mara lafiyan, haka ma ake bukatar fahimtar matsalar tattalin arziki kafin a fara warkar da ita.
“Abin da Shugaba Tinubu ya yi shi ne ya daidaita marar lafiyan, amma ban tabbatar ko ya kai ga gano matsalar ba. Don haka mara lafiyar ba zai mutu nan da nan ba, amma kuma ba a samo maganin cutar shi ba.
“Ba a gano ciwon da ke damun mara lafiyan ba, amma a matsayinsa na likita, yana daukar wasu matakai. Wasu daga cikin matakan ma sun kara ciwon mara lafiyar, amma sannu a hankali likitan yana samun nasara a wasu bangarorin, wanda hakan ke sa wasu su yi tunanin cewa mara lafiyan na kan hanyar warkewa,” in ji Adebayo.