An Ware Sama Da Naira Biliyan 1.5 Don Fara Aiki A Sabon Kamfanin Injinan Noma Na Jigawa
Published: 18th, March 2025 GMT
A yunkurin da gwamnatin jihar Jigawa ke yi na sauya fasalin harkar noma, majalisar zartaswa ta jihar ta amince da ware sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyar domin fara aiki da sabon Kamfanin injinan noma na jihar.
Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, an kafa kamfanin ne domin rage tsadar sarrafa kayayyakin amfanin gona a fadin jihar.
Ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da fitar da sama da naira miliyan dari tara da sittin da tara domin ci gaba da aiwatar da ayyukan kamfanin injinan noma.
Ya ce, wannan amincewa ta hada da biyan harajin kwastam da kudaden haraji na gwamnati kan kayan aikin injinan noma da kuma sassan gyara da aka sayo daga kasar Sin.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana cewa, majalisar ta tattauna kan wani kudirin doka da ya shafi kafa Asusun Tallafin Ibtila’in Ambaliyar ruwa na Jihar Jigawa.
Kwamishinan ya kara da cewa, amincewar ta yi daidai da kudirin Gwamna Umar Namadi na kawo dauwamammen mafita kan matsalolin ambaliya a jihar.
Ya ce, bayan tattaunawa, majalisar ta amince da kudirin dokar tare da mika shi zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sa-kai aƙalla 100 da jami’an tsaro 30 sun mutu a bakin aiki a Katsina —Gwamnati
Sama da mutum 100 daga cikin jami’an tsaron al’umma da Gwamnatin Katsina ta samar ne suka suka mutu a yayin aikin karaɗe ’yan bindiga da suka addabi al’ummomin jihar.
Wannan ƙari ne a kan sojoji da kuma aƙalla jami’an ’yan sanda 30 da suka rasu a yayin aikin tabbatar da tsaron rayuwa da duniyoyin al’umma, a cewar ma’aikatar tsaron jihar.
Kwamishinan tsaron jihar, Nasir Mua’zu ya sanar da haka ne a martaninsa kan wasu rahotanni da ke yawo a kafofin sada zumunta, waɗanda ya ce ana amfani da su domin tayar da hankalin jama’a.
Mu’azu ya ce Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa yana yin iya bakin koƙarinsa wajen shawo kan matsalar ’yan ta’adda kuma ana samun nasara a kansu.
Kwamishinan ya ce lokacin da Gwamna Raɗɗa ya karbi shugabancin Jihar Katsina, ƙananan hukumomi aƙalla 24 ne ke fama da matsalar ’yan bindiga, amma kuma sakamakon haɗin kai da jami’an tsaro da kuma ƙirƙiro ƙungiyar ’yan sa-kai ta jihar, an yi nasarar murƙushe su a ƙananan hukumomi 11.
Mu’azu ya ce, matsalar ta kuma yi sauƙi a wasu ƙananan hukumomi tara, in banda Faskari da Ƙankara da Safana da kuma Matazu, da ke ci gaba da dama da hare-hare.
Ya bayyana cewa hakan ba ya nufin cewa gwamnati ta gaza, domin jami’an tsaro na iya bakin ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaron lafiya da duniyoyin al’umma a wuraren.
A cewarsa, duk da hatsarin da gwamnan ya yi kwanakin baya, bai daina tattaunawa da shugabannin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ba da ke jihar, domin shawo kan matsalar.
Don haka ya buƙaci haɗin kai daga kowanne ɓangare, musamman ganin yadda jami’an tsaron ke sadaukar da rayukansu wajen kare lafiya.